Hukumar Kula da Ababen Hawa ta Jihar Kano (KAROTA) ta ce daga ranar Asabar, 1 ga watan Janairun 2022 za ta fara kamen direbibin Adaidaita Sahun da ba su sabunta izinin tukinsu na sabuwar shekarar ba.
Shugaban hukumar, Baffa Babba Dan-Agundi ne ya bayyana hakan yayin wata zantawarsa da manema labarai a Kano ranar Juma’a kan ayyukan hukumar a shekarar 2021 mai karewa.
- Ministan Abuja ya kamu da COVID-19
- Ban ji dadin yawan gyare-gyaren da Majalisa ta yi wa kasafin kudin 2022 ba – Buhari
Sai dai ya ce hukumar za ta basu har zuwa karshen watan na Janairu don su sabunta izinin, yana mai cewa kamen zai zama tuni ne a wajensu.
A cewarsa, “Wadanda za su nemi sabon izini za su biya N18,000, masu sabuntawa kuma N8,000. Mun yanke shawarar fara kamen ne daga daya ga wata saboda ya zama tini garesu.”
Shugaban ya kuma ce daga ranar ta daya ga wata, jami’an hukumar za su fara kama direbobin da ba su saka na’urar rage gudu ga ababen hawansu ba, sannan ta damka su ga Hukumar Kiyaye Hadurra ta Kasa (FRSC).
Bugu da kari, ya ce, “Daga yanzu kuma, za mu fara kama tirelolin da ke bin titunan da ba nasu ba a Jihar Kano. Sannan kuma dukkan masu ababen hawan da ke bin hannun da ya kamata masu yin kwana su bi ba a babbar hanya, za mu fara kama su. Haka ma masu bin hannun da ba nasu ba a titi mai hannu daya, su ma za mu fara kama su.”
Baffa ya kuma ce cikin shekarar 2021, hukumar ta KAROTA ta dauki sabbin ma’aikata 1,000, sannan ta kara yawan motocinta aikinta daga guda uku rak zuwa 60, sai kuma sabbin babura guda 50 da ta saya.
Ya kuma ce hukumar ta kama barayin yara da na waya da ma sauran kaya daban-daban da suke fakewa da tukin Adidaita Sahu wajen yi wa mutane sata, kuma akasarinsu an kai su kotu.