Kamfanin Mai na Kasa (NNPC) ya sanar da samun ribar Naira biliyan 37.5 a cikin kwana 30 a watan Satumban 2021.
Ribar da kamfanin ya samu ya karu da kashi 352 cikin 100 ke nan idan aka kwatanta da ribar N8.29bn da ya samu a watan Agustan shekarar.
- Gobara a tashar nukiliya; fararen hula na barin biranen da Rasha ta kwace
- Uwargida ta kashe miji a daren kwanan amarya
Babban Manajan Sashen Hulda da Jama’a na NNPC, Garba Deen Muhammad, ya bayyana cewa, kudaden shigar da NNPC ya samu, idan aka kwatanta da watan Agustan 2021 ya ragu da N191.90bn zuwa N450.45bn; Kashe kudade kuma ya ragu da zuwa N412.92bn.
Kudaden da aka samu daga danyen mai da iskar gas a watan Satumban ya karu zuwa Dala da 348.63 daga Dala miliyan 224.29 da aka samu a watan Agusta.
NNPC ya samu Dala miliyan 8.38 daga danyen mai, Dala miiyan 55.25 daga iskar gas sai kuma da Dala miliyan 285 na sauran kudaden da NNPC ya samu.
Jimlar ribar fitar da danyen mai da iskar gas daga watan Satumba 2020 zuwa Satumba 2021 Dala biliyan 2.03.
A bangaren samar da man fetur, NNPC ya ce an samar da lita biliyan 1.39 a watan, kusan lita miliyan 46.31 ke nan a kowace a rana a watan.
An samar da iskar gas da yawanta ta kai cubic feet biliyan 208.35 a watan, wanda ke nuna a kullum ana fitar da kimanin cubic feet miliyan 6,945.15 na iskar gas.
Daga watan Satumba 2020 zuwa Satumba 2021, an samar da iskar gas mai yawan kai cubic feet biliyan 2,862.36, kusan cubic feet milyan 7,250.16 ke nan a kowace rana.