✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Wayoyi Miliyan 25 Aka Sace Cikin Shekara 1 a Najeriya – NBS

Rahoton, ya kuma nuna cewa sama da mutum miliyan 17 ne, suka rasa wayoyinsu a tsakanin wannan lokacin.

Wani rahoto da Hukumar Ƙididdiga ta Ƙasa (NBS), ta fitar, ya nuna cewa an sace wayoyin salula sama da miliyan 25, daga watan Maris ɗin 2023 zuwa Afrilun 2024.

Rahoton, ya kuma nuna cewa sama da mutum miliyan 17 ne, suka rasa wayoyinsu a tsakanin wannan lokacin.

Wannan na nufin cewa a cikin duk wayoyi 10 da mutane ke amfani da su, an sace guda bakwai a shekarar.

NBS, ta kuma ce an fi samun satar wayoyi a gidaje da wuraren taruwar jama’a, kuma kashi 11.7 ne kacal na waɗanda aka yi wa satar suka kai wa ’yan sanda rahoto sannan suke kuma samun taimako.

Rahoton, ya kuma bayyana cewa ƙasa da kashi 10 na laifin satar wayoyi ne, suka kai gaban ’yan sanda, saboda dalilai daban-daban.

“A matakin ‘yan ƙasa kuwa, kashi 21.4 na ’yan Najeriya ne, suka ce an aikata musu laifin da ya saɓa wa doka, kuma satar waya na daga cikin manyan laifukan, inda yake da kashi 13.8,” in ji rahoton.