✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Watan gobe za a dawo haska shirin Labarina

A ranar 2 ga Yuli ce za a ci gaba da haska shirin fim din har a YouTube.

A ranar 2 ga Yuli ce za a dawo domin ci gaba da haska fitaccen shirin fim mai dogon zango na Labari zango na uku.

Daraktan shirin, Aminu Saira ya sanar da hakan a shafinsa na Instagram, cewa, “In sha Allah daga biyu ga watan July 2/7/2021 Labarina zango na uku zai fara zuwa muku a kowace ranar Juma’a da karfe 9 na dare zuwa 10 na dare, a tashar Arewa24 da Tambarin Hausa.”

Sai dai ba kamar yadda aka saba da nuna shirin a talabijin kadai ba, daga zango na ukun za a fara haska shirin a kafar YouTube.

Aminu Saira din ne ya sanar da hakan, inda ya ce, “ga masu kallo a internet kuma za su rika samunsa a tashar YouTube dina mai suna Saira Movies. Muna kara godiya gare ku.”

Labarina shiri ne da ya dauki hankali mutane da dama, wanda tun bayan kammala zango na biyu, aka tafi hutu na wani lokaci, aka yi ta dakon dawowar shirin.

Haka ma, a baya wasu daga cikin masu kallon fim din sun yi ta kira da a rika nuna musu shirin a YouTube, wanda za a iya cewa yanzu an amsa musu.