✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Watakila Aaron Ramsey ba zai buga wasan Arsenal da City gobe ba

Watakila dan kwallon tsakiya na kulob din Arsenal da ke Ingila Aaron Ramsey ba zai samu damar yin wasa a tsakanin kulob dinsa da na…

Watakila dan kwallon tsakiya na kulob din Arsenal da ke Ingila Aaron Ramsey ba zai samu damar yin wasa a tsakanin kulob dinsa da na Manchester City a gasar rukunin Premier na Ingila a gobe Asabar ba saboda raunin da ya samu.
Kocin Wales Chris Coleman ne ya sanar da jin ciwon dan kwallon a wasan da kasar Wales ta buga da ta Andorra a gasar neman zuwa gasar cin kofin Nahiyar Turai Euro 2016 da kasashen biyu suka yi a ranar Talatar da ta wuce.
Wales ce ta samu nasara a wasan da ci 2-1 kuma dan kwallon Real Madrid Gareth Bale ne ya zura kwallayen biyu.
Wannan shi ne karo na 44 da Andorra take yin wasa a jere ba tare da ta samu nasara ba kuma shi ne karon farko da ta jefa kwallo daya a raga a dukkan wasannin.