Wani memba a Hukumar kula da kwallon kafa ta duniya FIFA wanda ya ki a ambabci sunansa ya shaidawa jaridar Welt am Soontag a ranar Litinin da ta wuce cewa mai yiwuwa Hukumar ta kwace gasar cin kofin duniya daga wajen katar wacce aka amince tun farko ta dauki nauyin gasar a shekarar 2022 saboda wadansu matsaloli da suka dabaibaye kasar.
Ya ce a zaman da kwamitin lura da gasar zai yi a wannan shekara, alamu sun nuna da wuya ba a kwace gasar daga katar an ba wata kasa daban ba musamman ganin yadda hukumar ke ta samun koke-koke a kan yada ta amince wa katar daukar nauyin gasar tun farko. Ya ce idan hakan ta yiwuwu akwai lokaci isasshe da za a iya mayar da gasar wata kasa ba tare da an samu matsala ba.
A shekarar 2010 ce dai Hukumar FIFA ta amince wa katar a matsatyin kasar da za ta dauki nauyin gasar a shekarar 2022.
Daga cikin matsalolin da katar ke fuskanta dangane da shirye-shiryen da take yi na daukar nauyin gasar a yanzu sun hada da yadda akalla mutane 400 kwararrun injiniyoyi da ma’aikatan gine-gine da aka dauko hayarsu daga sassan duniya da suka rika haduwa da hadururruka daban-daban a yayin gudanar da ayyukansu da hakan ta sa wata jarida mai suna Obserber da ke kasar ta yi sharhi a ranar Lahadin da ta gabata kuma hakan ya tayar da hankalin al’ummar da ciki da wajen kasar.
Haka kuma masana harkar kwallo sun yi ta kwakwazon yadda aka amincewa kasar daukar nauyin gasar duk da irin yanayin zafin da kasar za ta fuskanta a lokacin da za a gudanar da gasar a tsakanin watannin Yuni da Yuni na kowace shekara.
Tuni Hukumar FIFA ta bakin Sakatare-Janar Jerome balcke ta tabbatar cewa ko da ba a kwace gasar daga kasar ba tilas ne a canza lokaci gudanar da ita daga watan Yuni zuwa lokacin hunturu saboda yayin zafin da ake fama da shi a kasar.
Hukumar ta ce hakan kuma zai shafi gasar rukuni-rukunin kasar da kuma gasar Olamfik ta 2022 da ake sa ran kasar za ta dauki nauyi kuma hakan zai sa da wuya gidajen Talabijin wadanda ke da alhakin daukar nauyin gasar su amince saboda matsalalolin da za su fuskanta.
…Watakila a kwace gasar cin kofin duniya na 2022 a wajen katar
Wani memba a Hukumar kula da kwallon kafa ta duniya FIFA wanda ya ki a ambabci sunansa ya shaidawa jaridar Welt am Soontag a ranar…
