✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Press To Play

Wata ta sake yin batanci ga Annabi a Maiduguri

Masu zanga-zangar dai na neman dole a hukunta wacce ta yi zagin

An fara zaman dar-dar a Maiduguri babban birnin Jihar Borno, bayan wasu sun fara zanga-zanga kan wata mai suna Naomi da ita ma ta zagi Annabi Muhammad (S.A.W) a shafinta na Facebook.

Daruruwan masu zanga-zangar dai sun mamaye barikin sojoji na Garrison da ke birnin da safiyar Litinin.

Sun dai kona tayoyi tare da rufe mashigar barikin, inda nan ne aka ce Naomin take zaune, inda suka bukaci sojojin su fito da ita.

Lamarin dai ya tilasta wa Kwamandan barikin ya fito ya yi wa masu zanga-zangar jawabi tare da rokon su su kwantar da hankula.

Daya daga cikin jagororin zanga-zangar, Umar Babagana, ya shaida wa Aminiya cewa matar da ta wallafa kalaman batancin tana zaune ne tare da wani soja a cikin barikin.

Ya ce, “Mun san ta a nan yankin, kuma lokacin da ta wallafa sakon, mun bukaci a kamata a hukunta ta ko mu dauki matakin da ya dace.”

Naomi dai a cikin sakon da ta wallafa ta nuna goyon bayanta ga Deborah Samuel, dalibar da aka kashe a Sakkwato bayan ita ma ta zagi Annabin, sannan ita ma ta zage shi a cikin sakon.

Sai dai sojoji da ’yan sanda sun tarwatsa masu zanga-zangar kuma abubuwa sun fara daidaita, ko da yake yanzu an girke jami’an tsaro a yankin don kaucewa sake barkewar tarzoma.