✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Wata mata ta sace ’yar makwabciyarta

Wata mata ta sace ’yar makwabciyarta bayan ta yaudari mahaifiyar yarinyar a Fatakwal, Jihar Ribas.

Wata mata ta sace ’yar makwabciyarta bayan ta yaudari mahaifiyar yarinyar a Fatakwal, Jihar Ribas.

Makwabciyar ta tsere da yarinyar mai shekara tara ce ta hanyar yaudararar maifiyar yarinyar da neman ’yar ta taimaka mata da wasu aikace-aikace.

Mahaifiyar yariyar, Favour Amaechi, ta shaida wa Aminiya cewa ce daga nan ne matar ta tsere da ’yarta zuwa inda ba a sani ba.

Ta bayyana cewa makwabciyar ta nemi ta bar ’yarta ta taya ta harkokin kasuwanci a yankin Mie 3 da ke Fatakwal, inda ta yi amfani da damar ta tsere da yarinyar.

“Ta zo gidana ta roke ni da in bar ’yata ta taimaka mata a kan kananan sana’o’inta, na amince na bar ’yata ta bi ita, sai ta ba da adireshin wurin da take zaune, sai daga baya na gano cewa ta yi layar zana.

“Mun yi kokarin gano ita da ’yata amma ba mu samu ba, sai na nemi wani abokina da ya taimaka min wajen gano ta, daga karshe muka same ta a waya, amma ta shaida wa abokin nawa da ya kira ta cewa in hakura da ’yata ko kuma in kai rahoto ga ’yan sanda,” inji ta.

Ta ce daga baya makwabciyar ta shaida wa dan sandan da ya kira ta daga Caji Ofis na Ada George cewa ta koma da zama a wani kauya a Jihar Anambra tare da yarinyar.

Wakilinmu ya tuntubi Jami’in Hulda da Jama’a na Rundunar ’Yan Sandan Jihar Ribas, SP Grace Iringe Koko, kan lamarin, amma ta ce za ta tuntube shi daga baya.