’Yan sanda sun yi nasarar kama wasu mutane biyu da ake zargi da laifin yi wa wata yarinya ‘yar shekara 12 fyaɗe a kauyen Jalingo da ke Ƙaramar Hukumar Tarmuwa a Jihar Yobe.
Hakan na ƙunshe ne cikin wata sanarwa da kakakin rundunar ‘yan sandan jihar, SP Dungus Abdulkarim, ya fitar a Damaturu ranar Litinin.
- Gwamnati ta raba wa mata tallafin awakai na N5bn a Katsina
- Yadda na yi wa budurwar da muka haɗu a Facebook gunduwa-gunduwa —Matashi
Ya ce lamarin ya faru ne da misalin ƙarfe 3:30 na yammacin ranar 15 ga watan Fabrairu, inda waɗanda ake zargin suka kai yarinyar wani kango a jeji suka keta mata haddi.
Rahoton na cewar, “Hedikwatar ‘yan sandan jihar reshen Ƙaramar Hukumar Tarmuwa ta cafke waɗanda ake zargin da suka haɗa baki tare da yi wa yarinyar ‘yar shekara 12 fyade, inda suka ji mata munanan raunuka.”
“Kamar yadda majiyar ke nunawa tuni wannan yarinya ta samu kulawa cikin gaggawa, yayin da aka miƙa waɗanda ake zargin zuwa sashin binciken manyan laifuka na jiha (SCID) da ke Damaturu domin gudanar da bincike mai zurfi akan su,” in ji Abdulkarim.
Haka nan a wani samame da aka yi, kakakin ya ce an kuma kama wasu ɓata gari uku a unguwar Alimari da ke Damaturu bisa zargin ɗauke wani babur tare da lalata shi kwanan nan a unguwar Abbari da ke cikin birnin na Damaturu.
A cewarsa, waɗanda ake zargin sun ɓoye babur ɗin ne da wasu kayayyaki a wani gini da ba a kammala ba a yankin.
Ya ce jami’an nasu da ke aiki a ofishin ‘yan sanda na A Divisional, sun kai farmaki gidan tare da cafke waɗanda ake zargi da aikata laifin satar babur ɗin.
Har ila yau, SP Abdulkarim ya ce hedikwatar ‘yan sanda ta Gujba tare da haɗin gwiwar ‘yan banga sun ceto wani matashi daga hannun masu garkuwa da mutane a ƙauyen Daddawel.
Ya ce matashin da aka yi garkuwa da shi a ranar 12 ga watan Fabrairu, ya shakami iskar ’yanci ne bayan wani artabu tsakanin masu garkuwar da ‘yan sanda da ‘yan sa kai, lamarin da ya tilasta wa masu laifin gudu suka bar wanda aka yi garkuwar da sauran kayayyaki ciki har da wata bindiga guda ɗaya.
Abdulkarim ya ce kwamishinan ‘yan sandan jihar, Garba Ahmed, ya yaba da ƙoƙarin jami’an rundunar, inda ya ba da tabbacin ɗorewar yaƙi da miyagun laifuka a jihar.