✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Wata mata ta haifi ’yan hudu

A makon da ya gabata ne wata mata mai suna Malama Habiba ta haifi ’ya’ya hudu a lokaci daya, uku maza, mace daya, a asibitin…

A makon da ya gabata ne wata mata mai suna Malama Habiba ta haifi ’ya’ya hudu a lokaci daya, uku maza, mace daya, a asibitin kwararru da ke Sakkwato, matar ta haifi yaran ba wata matsala a gare su da ita kanta ba, inda ta bayyana wannan a matsayin wata kyauta ta musamman da Ubangiji ya ba su a wannan lokaci.

Malam Isah Ibrahim Kwannawa shi ne mahaifin ’yan hudun, a zantawarsa da manema labarai a ranar  jiya Alhamis  da aka bikin sunan jarirai ’yan hudun,  ya gode wa Allah da kyautar da Ya yi masa, tare dab a da tabbacin cewa zai yi tsaye wajen renon yaransa ta hanyar musulunci har karshen rayuwarsa. An dai  bai wa yaran sunan Abubakar da  Umar da Usman da Fatima.

    Malam Isah wanda talaka ne da ba ya wata sana’a sai noman rani da damina, ya kwashe tsawon shekara takwas da matarsa, sun samu zuriya ta ’ya’ya shida a yanzu,  a haihuwar  matarsa ta farko ta haifa masa tagwaye, yanzu kuma ta haifi ’yan hudu a haihuwarta ta biyu.

‘‘Habiba ’yar baiwa ce, muna tare da ita shekaru takwas, a haihuwar farko ta Haifa min ’yan biyu, bayan shekaru bakwai sai ga ’yan hudu, sun zo da goshi sosai, na samu gudunmuwa a kansu da ban taba zato ba, ga manyan mutane sun so gidana a yau (jiya alhamis) don shedar sunan yaran, wannan haihuwa arziki ce na tabbata,’’ a cewar Malam Isa Ibrahim.

Ya kara da cewa, bai taba jin damuwa ba tun lokacin da matarsa take da juna biyu, kuma ba ta hadu da wani cikas ba har ta haihu, yaran sun mayar da shi mutumin da ya samu daukaka a jihar Sakkwato, inda abokai da dangi suke ta kiransa don taya shi murna.

Isah Kwannawa ya gode wa ga gwamnatin jihar Sakkwato kan alkawarin daukar  nauyin karatun yaran, ganin shi talaka ne da ke rayuwa a kauye kuma yana da burin yaran su yi karatu don su amfani jama’a.

Gwamnatin Sakkwato za ta dauki nauyin karatunsu

Gwamna Aminu Waziri Tambuwal  na jihar Sakkwato ya bai wa Malama  Isah Kwannawa da matarsa Habiba Isah tallafin  kudi Naira dubu dari biyar da buhun shinkafa goma da madarar yara da atamfofi da kayan yara na sawa da na wanka da katifun yara da gidan sauro, an mika kayan ne  a garin Kwannawar Tangaza a cikin karamar hukumar mulkin Tangaza. 

Kwamishinoni biyu ne suka gabatar da sakon Gwamnan  a ranar Litinin da ta gabata, Kwamishinan jin dadin jama’a Alhaji Sirajo Gatawa da na lafiya Dakta Balarabe Kakale.  

Kwamishinan na jin dadin jama’a ya taya iyayen murna, ya ce Tambuwal na kokari ganin ya kula da jin dadin al’umarsa a kodayaushe, don haka ya tura su su gabatar da tallafi ga uwar yaran da maigidanta. 

Ya kuma yi musu albishiri da cewa gwamnatin jiha za ta dauki nauyin  kula da jariran gwargwadon hali, kuma in sun isa zuwa makaranta za a dauki nauyin karatunsu tun daga firamare har zuwa jami’a.  

Shi ma Kwamishinan lafiya Dakta Balarabe Kakale ya yi kira ne ga iyayen da su tabbatar  an yi wa yaransu allurar rigakfin kamuwa da cututtukan yara don samun ingantacciyar lafiya. ‘Mutanen gari kuma na roke ku da ku rika bari ana yi wa yaranku allurar rigafi saboda ba ta da wata illa a jikin yara,’ a cewarsa. 

Shugaban karamar hukumar mulkin Tangaza da mahaifin ’yan hudun sun gode wa Gwamnanjihar Sakkwato kan karimcin da ya yi.

Shi ma Sanata Aliyu Magatakarda Wamakko Mai wakiltar Sakkwato ta Kudu a Majalisar dattiijai kuma tsohon Gwamnan jihar Sakkwato, ya bai wa iyalan ’yan hudun  ragunan suna guda hudu, watau kowane yaro rago daya ke nan. 

A watan da ya gabata ma gwamnatin jahar  ta ba da tallafin  kayan abinci da gidan sauro da kudi Naira dubu dari biyar  ga Malam Lawwali mai shinkafa Illela, wanda matarsa Malama Shafa’atu  ta haifi masa ’yan hudu a karamar hukumar  Illela ta jihar Sakkwato. Mai jego da jariran, wadanda duka mata ne, suna cikin koshin lafiya.

Kwamishinan ma’aikatar jindadin jama’a Alhaji Sirajo Gatawa ne kuma ya gabatar da kayan ga iyalan ’yan hudun a gidansu da ke cikin garin Illela, a lokacin gabatar da kayan Kwamishinan Ya bayyana  Gwamna Aminu Waziri Tambuwal ne ya umurce Shi da ya gabatar da wannan tallafin biyo bayan sanar da Shi da aka yi game da haihuwar.