✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

…Wata kuma ta kaure a tsakanin Ministan Mai da Shugaban Kamfanin NNPC

Takaddama ta kaure a tsakanin Minista a Ma’aikatar Albakatun Man Fetur, Mista Ibe Kachikwu da Shugaban Kamfanin Mai na kasa (NNPC), Injiniya Maikanti Baru. Wata…

Takaddama ta kaure a tsakanin Minista a Ma’aikatar Albakatun Man Fetur, Mista Ibe Kachikwu da Shugaban Kamfanin Mai na kasa (NNPC), Injiniya Maikanti Baru.

Wata wasika da Ministan ya aike wa Shugaban kasa Muhammadu Buhari, ya zargi shugaban Kamfanin NNPC da “yin ba daidai ba da kuma rashin da’a.”

Wasikar wadda aka yayata a kafafen sadarwa na Najeriya, ta ce Ministan ya zargi MaiKanti Baru da daukar manyan ma’aikatan kamfanin man da ba da kwagilolin da suka haura Dala biliyan 20.

“Sabanin yadda doka ta bukata cewa sai ya nemi yardar Ministan,” wanda shi ne Shugaban Hukumar Gudanarwar Kamfanin NNPC, kuma mai sanya ido a kan kamfanin. 

Ministan ya ce, “Da na nemi sanin abin da ya sa shugaban NNPC din yin hakan, sai ya gaya masa cewa Shugaban kasa ne ya amince da daukar ayyukan da kuma ba da kwagilolin.”

Tuni Majalisar Dattawa ta kafa wani kwamiti da zai binciki zarge-zargen da Ministan ya yi a cikin wasikar. Sai dai Fadar Shugaban kasa da kuma Kamfanin NNPC, sun yi gum da bakinsu kan wannan takaddama.

Sai dai wata majiya ta ce, an shirya Shugaban kasa zai gana da Minista a Ma’aikatar Man Fetur din a jiya Alhamis, sai dai har zuwa hada wannan rahoto ba mu samu bayanin ko an yi ganarwa ko ba a yi ba, balle abin da suka tattauna.

Jami’an gwamnatin Buhari da dama sun yi takaddama a tsakaninsu, inda a baya aka samu haka a tsakanin Ministan Shari’a, Abubakar Malami da Mukaddashin Shugaban Hukumar EFCC, Ibrahim Magu, sai dai dukansu sun musanta zargin. Kuma, an taba samun takaddama a tsakanin Ministan Lafiya da Shugaban Hukumar Inshorar Lafiya (NHIS), wadda ta kai ga dakatar da shugaban hukumar da kuma kafa kwamitin bincike a kan lamarin, duk da Majalisar Wakilai ta hana yin haka.