✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Wata dalibar Chibok ta sake tserewa daga hannun Boko Haram

An mika dalibar ga gwamnatin Jihar Borno.

Wata daga cikin ‘yan mata 270 da aka sace a makarantar sakandiren Chibok da ke Jihar Borno, Hassana Adamu ta kubuta daga hannun Boko Haram.

A daren 14 ga watan Afrilun 2014 ne mayakan Boko Haram suka afka wa makarantar Sakandiren Mata zalla da ke garin Chibok tare da sace dalibai fiye da 200.

  1.  Kotu ta daure masu kwacen waya shekara 7 a kurkuku
  2. Mahara sun kai farmaki ofishin ’yan sanda a Anambra

Wata sanarwa da Mallam Isa Gusau, mai ba gwamnan shawara na musamman kan harkokin sadarwa ya fitar, ta ce sojoji ne suka mika dalibar ga Gwamna Babagana Zulum a ranar Asabar a garin Gwoza.

Bayanai sun ce sojojin sun mika wa gwamnan Hassana bayan ta gabatar musu da kanta kamar yadda wata dalibar ta yi makonnin da suka shude.

Dalibar, tare da ’ya’yanta biyu, wanda Kwamandan rundunar soji ta 26 Birgediya-Janar D. R. Dantani ya mika su ga gwamnatin jihar.

Ana iya tuna cewa, wata daga ’yan matan Chibok da aka sace, a ranar 28 ga Yulin 2021 ne Ruth Ngladar Pogu ta mika kanta ga sojojin Najeriya ita da wani mutum da ta ce mijinta ne da ta aura a lokacin da suke tsare