✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Wata 9 matata tana lakada mani duka

Matarsa tana gallaza masa tare da jibgar sa a duk lokacin da suka samu sabani a tsawon lokacin da suke tare a matsayin mata da…

A yawaicin lokuta, duk a inda ka ji an ci zalin wani har ta kai ga duka a zaman aure, za ka taras namiji ne.

Sai ga shi a wani juyin al’amari na aljabi aka samu wannan magidancin da matarsa ta rika lakada masa duka tsawon wata tara.

Mista Moses Onome shi ne wanda wannan al’amarin ya faru da shi a yayin zaman aurensu da matarsa wacce take gallaza masa tare da jibgar sa a duk lokacin da suka samu sabani a tsawon lokacin da suke tare a matsayin mata da miji.

A hirar da ya yi da Saturday Trust, Mista Moses ya bayyana yadda ta kwashe tsakaninsa da matar tasa, wacce aka daura musu aure bayan sun sha soyayya, wadda masu iya magana kan ce, ruwan zuma ce, amma ga Mista Moses ta zama ruwan madaci bayan daura auren nasu.

Mista Moses ya ce hakika farkon soyayyarsu ya lura da cewa matar tasa na da saurin fushi kuma idan ranta ya baci, takan yi wasu abubuwa na tashin hankali amma ba ta duka.

A lokacin ma koda sun samu sabani, idan ta yi fushi, tafiya take yi ta rabu da shi, har sai ta sauko tukunna, sannan su daidaita.

Amma ba ta taba kai masa bugu ba ko da wasa.

Amma da aka yi auren sai abubuwa suka sauya, inda halinta ya fito fili, inji shi.

“Tana da tsananin fushin da idan ta hassala, a sakamakon wani sa-in-sa tsakaninmu ko musu, sai ta shiga jifa na da abubuwa, ko kuma ta kama farfasa su da tarwatsa komai cikin fushi.

“Idan na yi kokarin hana ta ko kare kaina, sai ta juyo kaina da duk abin da ta samu na duka, ko sara, ko kuma suka.

“Ita babu ruwanta.”

Moses ya ce, wani lokacin yakan yi kokarin ramawa amma hakan sai ya zama dole.

Idan kuma ya rasa yadda zai yi. Amma da alama ita take galaba a kansa, kamar yadda ya nuna a hirar.

Matar tasa takan yi nadamar abin da ta aikata bayan ta sauko daga kan dokin zuciyar da ta hau, ta kuma huce.

A cewar sa, shi ma yakan rarrashe ta, tare da yi mata ’yan nasihohi da kuma jan hankalinta kan abin da ta aikata.

Kai ka dauka ta yi nadama kuma ba za ta sake aikata haka ba amma ba haka ba ne.

Wani abu na sake hada su sai ta koma gidan jiya.

Da ya yake an ce, jiki ma gayi inji ’yan magana, kasancewar tsawon lokaci matar tasa tana yi masa haka, sai Mista Moses ya ce ya gaji, domin da alama halinta ne haka, ba kuma za ta iya dainawa ba.

Domin a cewarsa, yau da gobe ta sa makwabta da sauran mutane kowa ya san halinta, ballanatana ’yan uwa da kuma danginsaa.

“Ni dai kam ba na iya fada wa kowa irin azabar da nake sha a hannunta, don haka muka rabu bayan watanni 9 kacal da aurenmu,” inji Moses.

Ya ce sun rabu ne, domin gudun abin da zai iya faruwa nan gaba, domin idan ta zo da karar kwana, za ta iya halaka shi.

A cerwar sa.