A yau, 26 ga watan Satumba, 2023 ake cika wata biyu bayan sojojin Jamhuriyar Nijar sun hambarar da gwamnatin Shugaba Mohamed Baozum.
A tsawon wata biyun nan, sojojin karkashin jagorancin Janar Abdourahamane Tchiani a gefe guda, da kuma Kungiyar Raya Tattalin Yammacin Afirka (ECOWAS) da ma wasu manyan kasashen a daya bangaren na ta tayar da jijyoyin wuya kan shugabancin kasar.
- Yadda sojoji suka ceto 10 daga cin daliban jami’a da aka sace a Zamfara
- Tagwaye sun kirkiri rusho mai amfani da ruwa a Kano
ECOWAS da sauran kasashen, cikin har da babbar kawar gwamnatin Bazoum kuma tsohuwar uwar gijiyar Nijar, wato Faransa da kungiyoyin ke neman a dawo da shi kan mulki, sojojin kuma suka ce ba za ta sabu ba.
ECOWAS ta yi barazanar amfani da karfin soji wurin dawo da Bazoum, a yayin da Gwamnatin Janar Tchiani ta ce bismillah — lamarin da har yanzu ake ta kai ruwa rana a kai.
Kungiyar ta kaste hulda da gwamnatin sojin tare da kakaba musu takunkuman karya tattalin arziki, kafin daga bisani su fara hawa kan teburin tattaunawa.
Sojojin sun kuma yanke hulda da Faransa suka nemi ta kwashe sojojinta da jakadanta daga kasarsu, amma ta ce ba su isa ba, tunda su ba halastacciyar gwamnati ba ce.
– Wane tasiri takunkumin ECOWAS ya yi? –
Takunkumin ECOWAS ya sa har yanzu kasashen kungiyar da ke da iyaka da Jamhuriyar Nijar rufe iyakokinsu, duk da kasancewarta daya daga cikin kasashe mafiya talauci.
A sakamakon haka, Majalisar Dinkin Duniya (MDD) ta ce farashin shinkafa da masara da dawa da sauran hatsi a kasar ya yi tashin gwauron zabo.
Shugaban Kungiyar Masu Hada Magunguna ta kasar. Amadou Seyni Maiga, ya ce, “Karancin magunguna ya kai kashi 30-55 cikin 100 a ranar 19 ga watan Satumba.”
MDD ta sanya baki domin “ECOWAS ta sassauta da nufin samar da kayan jinkai, saboda ba sa isa cikin kasar da wuri” in ji jami’in MDD da ke kula da ayyukan jinkai a Nijar Louise Aubin.
Sai dai duk da haka, Nijar na ci gaba da gudanar da harkokin kasuwanci da makwabtanta irinsu Algeria, kuma har yanzu takunkumin karya tatttalin arzikin da aka sanya mata bai sa masu juyin mulkin da magoya bayansu sun girgiza ba.
Sannan bayan kulla wata yarjejeniyar tsaro, Nijar ta dogara da manyan kawaye kuma makwabtanta Mali da Burkina Faso — da su ma tun da farko sojoji suka kwace mulki — wajen tunkarar duk wata barazanar tsaro.
– Ina aka kwana tattaunawa? –
ECOWAS dai ta yi wa masu juyin mulkin Nijar barazanar amfani da karfin soji domin ganin an dawo da Bazoum kan kujerarsa, amma hakarta bai cim-ma ruwa ba.
Yanzu dai kungiyar ta yi gum kan matakin sojin nata, wanda ake ganin mai matukar hadari ne ga Nijar da ma yankin Yammacin Afirka.
A tsakanin daidaikun kasashen kungiyar kuma an samu rabuwar kai, sannan har yanzu ba a cim-ma wata kwakkwarar matsaya ba a tattaunawarta da sojojin Nijar.
Gwamnatin Janar Abdourahamane Tchiani dai ta ce tana bukatar wa’adin da ba zai wuce shekara uku ba domin dawo da tsarin dimokuradiyya a Nijar. Kungiyoyi da ke goyon bayansu na goyon bayan fiye da wa’adin da sojojin suka diba.
Wata majiyar diflomasiya ta ce, “da alama ECOWAS za ta dauki matsakaicin matsayi, amma ba za ta abince da shekara uku da sojojin suka bukata na gwamnatin rikon kwarya ba.”
– Shin Faransa ta saduda? –
Har yanzu dai Faransa ba ta ganin masu juyin mulkin a matsayin halastacciyar gwamnati. Su kuma sun matsa cewa sai ta bar kasarsu, a yayin da ita kuma take kokarin ganin Bazoum ya dawo.
Amma a ranar Lahadi Shugaban Faransa, Emmanuel Macron ya ce ya zama tilas kasarsa ta dauke jakadanta daga Nijar nan take, sannan sojojinta su biyyo shi a watanni masu zuwa.
Ya ce “Faransa ta yanke shawarar janye jakadanta da sauran jami’an jakandacinta a Nijar nan da sa’o’i masu zuwa.”
Sannan ya ce “nan da karshen shekarar nan” kasarsa za ta rufe ayyukanta na soji ta kuma kwashe sojojinta daga Nijar.
Shugabannin juyin mulkin Nijar dai sun yi na’am da hakan a matsayin wani mataki na samu cikakken ’yancin kasarsu.
– Shin tsaro ya inganta? –
Yankin Sahel da Nijar take dai ya shafe shekaru yana fama da hare-haren mayaka masu ikirarin jihadi.
Duk da komawar kasar hannun sojoji, mayakan sun ci gaba da kai hare-harensu, inda a wasu lokuta suka kashe sojoji.
Lamarin ta’addancin ya fi kamari a yankin Arewwa maso yammacin Nijar da ke iyaka da kasashen Mali da Burkina Faso.
– Ina makomar Bazoum? –
Har yanzu Mohamed Bazoum na tsare tare da dansa da matarsa a hannun sojojin da suka yi masa juyin mulki a fadar shugaban kasa.
A ranar Laraba lauyansa ya shigar ga kara Kotun ECOWAS yana neman ta umarci sojojin su sake shi tare da iyalansa, domin tsarewar tauye hakkokinsu na walwala ne.
Sojojin sun ce za su gurfanar da Bazoum kan zargin “cin amanar kasa”, kuma a ranar Alhamis suka ayyana wasu mutum 20 daga jami’an gwamnatinsa a matsayin wadanda ake nema ruwa a jallo.
Sojojin da suka ce sun kwace mulki ne saboda tabarbarewar tsaro da kuma yawaitar almundahana a kasar, sun kaddamar da hukumar yaki da rashawa a ranar Laraba, da nufin kwato dukiyar kasar da aka sace ko aka karkatar.
– Ina aka dosa? –
Bayan shafe makonni ana kai ruwa rana da kuma nuna adawa da Faransa da ECOWAS a Nijar, an fara muhawara kan harkokin siyasar kasar a cikin gida.
Daga cikin batutuwan da ake tattaunawa a kai kuwa har da gwamnatin magabacin Bazoum, Mahamadou Issoufou, daga 2011 zuwa 2021.
“A shekara 12 da suka wuce a kasar nan babu abin da ake yi sai sata da cutar jama’a. Don haka abu da ya fi komai muhimmanci shi ne a fara yin adalci,” in ji Clement Anatovi, wani wanda ke shirya tarukan al’umma a Yamai, babban birnin kasar.