✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Wasu ’yan sanda uku sun rasa aikin su a Legas

Rundunar ’yan sandan Jihar Legas ta kori ’yan sanda uku da ke aiki a rundunar, waɗanda aka same su da laifin sakaci da amfani da…

Rundunar ’yan sandan Jihar Legas ta kori ’yan sanda uku da ke aiki a rundunar, waɗanda aka same su da laifin sakaci da amfani da makami ta hanyar da ba ta dace ba.

A wata sanarwa da Kwamishinan ’yan sanda a Legas Edigal Imohimi ya fitar, ya shaida cewa ’yan sandan da rundunar ta kora sun haɗa da Sajen  Osaseri Saturday mai lamba 25759 da Sajen Segun Okun mai lamba 359075, sai  Kopur Adekunle Oluwarotimi mai lamba 496833; dukkaninsu da ke aiki a ofishin rundunar da ke shiyyar Amokoko. Sun kuma aikata laifin da aka kama su da shi ne a ranar Alhamis ɗin makon jiya, inda suka mayar da martani ta hanyar yin harbi ga wasu matasan da suka far masu da jifa da duwatsu da sanduna a unguwar Ifelodun d ake yankin Amukoko, lamarin da ya yi sanadiyyar mutuwar ɗaya daga cikin matasan tare da jikkata wasunsu. Dalili ke nan ya sanya aka kame ’yan sandan tare yin bincike, inda daga bisani aka sallame su daga aiki.

Kwamishinan na ’yan sandan ya yi kira ga manyan jami’an ’yan sandan da ke kula da shiyoyyin jihar da su dinga jan kunnen jami’an da ke aiki a ƙarƙashinsu, domin guje wa faruwar haka. Ya ce dole ne jami’an ’yan sandan su dinga lura wajan sarrafa makami a lokacin da suke tu’ammali da jama’a.