Ƙungiyar Ƙwadago NLC ta yi fatali da tayin naira 48,000 da Gwamnatin Tarayya ta gabatar a matsayin mafi ƙarancin albashin ma’aikata a ƙasar.
Mambobin ƙungiyar ta NLC a wannan Larabar su bayyana mamakin dalilin da gwamnati da mambobin kamfanoni masu zaman kansu ke tozarta su da abin da ta bayyana a matsayin tayi mai ban dariya.
- An gurfanar da Emefiele kan kashe N18.96bn wajen buga takardun kuɗi na N684.5m
- Kwastam ta kama man fetur na Naira miliyan 8.8 a Legas
Aminiya ta ruwaito cewa a yayin da Gwamnatin Tarayya ta miƙa tayin Naira 48,000, ‘yan ƙungiyoyi masu zaman kansu sun miƙa tayin N54,000.
Sai dai ƙungiyar NLCn ta bayyana adawartwa kan duk tayin da ɓangarorin biyu suka gabatar a wani taron tattaunawa da aka gudanar a babban Ofishin NLC na Labour House da ke Abuja.
Shugabannin ƙwadagon sun ce gwamnati ba ta gabatar da wasu bayanai da za su goyi bayan tayin da ta gabatar ba.