An yanke wa wani malamin makarantar sakandare, Ojo Ezekiel, hukuncin daurin rai da rai bisa samun sa da laifin yi wa wata yarinya ’yar shekara bakwai fyade.
Babbar kotun jihar Ogun da ke zamanta a Abeokuta, ce ta yanke wa Ojo Ezekiel mai shekara 47 bayan an fara gurfanar da shi bisa zargin a ranar 1 ga Yuli, 2022,
Lauya mai shigar da kara, Olusegun Olaotan, ya shaida wa kotun cewa mahaifiyar wadda aka yi wa fyade ne ta gano an ci zarafin ’yarta a lokacin da take mata wanka.
Bayan daukar lokaci ana mata tambayoyi ne yarinyar ta fada wa mahaifiyar yadda wanda aka yanke wa hukuncin ya yi lalata da ita.
- 1 daga cikin mutanen da aka cinna wa wuta a masallaci a Kano ya rasu
- Shari’ar Batanci: Abduljabbar ya kori lauyansa
Shaidar mai gabatar da kara ta uku (likita) ta tabbatar da jawabin mai gabatar da kara na biyucewar a yayin da ake duba wadda aka yi wa fyade, “an gano cewa an dan buda matancin yarinyar.”
Olaotan ya ce wadda aka yi wa fyaden ta ambaci sunan wanda ake tuhuma a matsayin wanda ya rika saka yatsansa a cikin al’aurarta.
Lauyan da ya shigar da kara ya bukaci kotun ta hukunta wanda ake kara domin an gabatar da wadatattun shaidu kuma tana da ikon da za ta iya kama shi da laifin fyade ta kuma hukunta shi.
A hukuncin da ya yanke, Mai Shari’a Abiodun Akinyemi, ya ce lauyan mai shigar da kara ya kafa hujjojin da ake bukata domin tabbatar da cewa wanda ake zargin ya aikata fyaden, don haka ya yanke masa hukuncin daurin rai da rai.