✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Wasu ’yan Arewa sun taba cewa in gaya wa Buhari kada ya sake yin takara – Zangon Daura

Mene ne ra’ayinka game da bayyana niyyar tsayawa takara da Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya yi kan zaben 2019? Na yi murna da jin haka,…

Mene ne ra’ayinka game da bayyana niyyar tsayawa takara da Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya yi kan zaben 2019?

Na yi murna da jin haka, domin na dade ban ga Shugaban da jama’a suke so kamar Muhammadu Buhari ba. Ana son sa ne domin gaskiyarsa da jajircewarsa da cika-fuska. Shi ya sa wata mujalla Drum Magazine ta ce yana da “daure fuska da gaskiya,” lokacin ya ya hau mulki a zamanin soja. Wannan ra’ayina ne ba na wata kungiya ba, kuma na tabbatar jama’a na murna da wannan jawabi. Tunda ya hau mulki a matsayin Shugaban kasa, an samu ingantuwar zaman lafiya, ya zo ne a lokacin da mutane ke matukar jin tsoro a masallaci da coci da kasuwa da jana’iza da tashar mota da sauransu. Buhari ba ya hau mulki ba ne don ya yi sata, sai domin ya gyara kasa, ta dawo bin doka a aikin gwamnati da shari’a da sauransu. Duk mai hankali ya san an samu canji daga irin salon mulkin gwamnatin baya. Buhari ya zo ne don ya ceci kasa, ba don ya yi wa kansa aiki yake neman tazarce ba, sai dai don ya tallafa wa kasa da jama’arta.

 Amma wadansu jagororin kungiyoyi suna cewa bai kamata ya nemi tazarce ba?

Dadin mulkin farar-hula shi ne an ba kowa damar ya furta ra’ayinsa koda soki-burutsu ne, kowa na iya ganin kurensa, amma ka kwatanta da mulkin da ya wuce na wasoso. Kafin zuwansa Najeriya na dab da rugujewa, sai Allah Ya ba shi mulki ya daidaita kasa inda yake yakar Boko Haram. Duk wanda ya ce kada ya nemi kuri’a ko tazarce, kila barawon dukiyar kasa ne ko kuma yana da laifi ne da ake bincikensa. Ni dai na ce sai Buhari!

 Amma da kai aka kafa Jam’iyyar PDP…

Da na yi PDP, amma a yanzu ni dattijo ne na bar siyasa, amma ina goyon bayan Buhari. Shekarar da ta wuce, wadansu mutane daga Arewa sun ziyarce ni suka ce sun zo su ba ni sako in je in gaya wa Buhari cewa kada ya yi takara. Sai na ce musu cewa wa zai iya kafa jam’iyyar siyasa ya kuma ci zaben Shugaban kasa a cikin wata 6 da kuri’u miliyan 12. Na san ya samu fiye da kuri’a miliyan 12, sai na ce su kawo min sunan mutum daya da za a iya kwatanta shi da Buhari, in sun kira sunan zan je in gaya masa kada ya yi takara. Sai suka ce in gaya wa Bola Tinubu cewa shi ma kada ya yi takara, sai na ce ina jiran su gaya min sunan mutum daya, sai suka watse.

 Me za ka ce game da kungiyoyin da suke kwakwazon adawa da Buhari, shin ko za su iya kada shi a zabe?

Ba za su iya kada Buhari a zabe ba. Su wane ne suke cikin wadannan kungiyoyi? Me suka yi a baya? Kowa na iya yin harigido (dariya), amma ’yan Najeriya sun waye, sau uku yana cin zabe ana dannewa amma daga baya duk da yawan kudinsu, suka fadi a zabe. Buhari ba ya da kudi, sai dai yana kwatanta gaskiya, shi ya sa jama’a suke son sa. 

 Wadansu na cewa shekarunsa sun haura shi ya sa yake aiki a hankali ba hanzari?

Yana mulki ne da lura da abin da kake yi, kuma mulkin dimokuradiyya ba mulkin soja ba ne, shi ya sa ya tura kasafin kudi zuwa Majalisar Dokoki ta kasa, sannan ya rage nasu ko su amince, ko su yi kwaskwarima duk da an shiga watanni a cikin shekarar. A lokacin ina karatu a Landan ake ta cewa Firayi Minista Harold Macmillan ya tsufa, sai ya ce yana da shekaru, amma shi matashi ne. Haka an zabi Morarji Desai a matsayin Firayi Minista a Indiya yana da shekara 82. A siyasa neman jagorori ake da za su yi wa mutum kamfe, in an ci zabe a samu wadansu amintattun wakilai su yi maka aiki don ba kowane abu ne za ka karanta ba. 

 Wace shawara za ka ba bangarorin gudanarwa da majalisa da shari’a don su hada kai su ciyar da kasa gaba?

Ya dace su hada kai don ciyar da kasa gaba. Bai kamata ra’ayin mutum ya fi na kasa ba ta hanyar yin muhawara da daukar ra’ayin wanda ya fi rinjaye.

 Kafin zaben 2015, Buhari ya yi kamfe ne a kan abubuwa uku: Magance cin hanci da inganta tsaro da tattalin arziki. Me zai yi kamfe a kai yanzu?

Tsaro babban abu ne. Ya ci nasarar matuka kuma in babu tsaro, ba abin da za ka iya yi. Kuma ko a kasashen da suka ci gaba ana samun matalolin tsaro a Turai da Amurka, inda ake harbe yara ’yan makaranta da garkuwa da mutane. kokarin Buhari ya sa kungiyar Tarayyar Afirka ta karrama shi.

 Mene ne ra’ayinka game da cewa dattajawa su mika mulki ga matasa?

(Dariya). Lokacin da Janar Babangida ya ce zai janyo matasa cikin mulki, na ce masa ya dace a koya musu mulkin tukunna kafin a mika musu mulkin. Daga baya shi da kansa ya yi da-na-sanin ba da mulki ga matasa, inda wadansu kansilolin ’yan shekara 18 ba su da aure, ba su da iyali, ba su da wani nauyi a kansu, suka koma suna raba wa jama’a kudin da ya kamata a yi aiki da su. Ni da marigayi Umaru Dikko muna da shekara 30 aka dauke mu aka tsunduma a cikin gwamnatin Birgediya Abba Kyari a Kaduna kuma muka yi kokari. A yanzu yawanci masu mulki matasa ne, ni dai na ta san ma shekara 80.