✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Wasu hotunan tarihi masu ban al’ajabi da aka manta da su

Hoton Usama Bin Laden yana dan gaye, da wasu kayatattun hotunan tarihi.

Akwai wadansu hotunan tarihi masu ban sha’awa da al’ajabi da aka manta da su a yanzu, amma kuma bai kamata a manta da su din ba.

Baya ga abin mamaki da hotunan ke dauke da shi, wasu daga cikinsu idan aka kalle su da kyau za a ga akwai hikima da darussa sosai a cikinsu.

Daga ciki za ku ga Usama Bin Laden yana dan saurayi ta ma sauran kayatattun hotuna:

Wannan wani cunkoson ababen hawa ne da aka yi a kasar Sweden, ranar 3 ga Satumbar shekarar 1967, ranar da aka sauya tsarin tafiyar ababen hawa daga tafiya ta hannun hagu zuwa hannun dama.

Mutane da dama sun makara zuwa wajen aiki a ranar sakamakon cunkoson ababen hawa da rashin sabon ya haifar.

A wannan hoton wasu mutum 25 ne suka cunkusa a cikin dakin kiran waya a kasar Afirkta ta Kudu, don su shiga kundin tarihin duniya na Guiness.

Saboda haka ne wasu dalibai 19 a kasar Birtaniya su ma suka cunkusa kansu a irin wannan dakin domin su kafa nasu tarihin.

Wannan shi ne ginin gidan abincin kwalama na kamfanin McDonald’s na farko a San Bernardino da ke Jihar Kalifoniya a kasar Amurka.

Kamfanin MacDonald’s dai ya shahara wajen sayar da kayatattun abinci da kayan kwalama na zamani, kuma yana da rassa a sassan duniya da dama.

A lokaci Yakin Duniya na Biyu turawa sun tsorata da Adolf Hitler, lamarin da ya sa suka shirya masa ta kowane bangare, hatta daliban kwaleji ba a bari ba. Wannan hoton daliban Kwalejin Eton ne da aka koya wa dabarun yaki a lokacin.

A da wannan dan dangalallen kayan shi ne kayan da ma’aikatan cikin jirgi ke sanyawa.

Ganin cewa bai kamata a sanya kayan wajen shiga cikin jama’a ba, ya sa a shekarar 1959, kamfanin sufurin jiragen sama na SAS ya sauya kayan zuwa wandanda ake amfani da su a yanzu.

 

Wannan kuma hoton wata mata ce ta sanya ’ya’yanta hudu a kasuwa sakamakon talaucin da ta fada bayan wani yaki da ya taba riskarta, ganin talauci ya dabaibaye ta ya sanya ta sa yaran a kasuwa.

 

Wannan hoton kuma dangin Usama Bin Laden ne tare da shi a 1970, lokacin da suka je hutu a kasar Sweden. Shi ne ke zagaye da jar alama.

 

Lokacin da daukar hoto ya fara tashe, iyaye da dama sun yi ta son ganin an dauki hoton ’ya’yansu kanana, amma yaran ba su zama don haka aka samo wata dabara kamar yadda kuke gani.

Wannan yaro ne yake zaune a kan doguwar kujera a bayyane, amma kuma a karkashin doguwar rigar, mahaifiyarsa ce a rufe tana rike da shi.

Zai  yi wuya ga mai kallon fim ya ce bai san kamfanin fina-finan Disney Studio ko tambarinsa ba. Wadannan mutane su ne ma’aikatan farko aka kafa kamfanin da su. An dauki wannan hoton ne a ranar farko da suka bude kamfanin.

A shekarun 1940 zuwa 1950 mutane sun mayar da hankali sosai a kan gasar tseren yara, wannan ya sa kamfanin Diaper Derby yake shirya gasar a kowacce shekara.

Wannan hoton an dauke shi ne lokacin da ake tsaka da gasar. A kan ajiye wani abin wasa da zai ja hankalin yaran a karshen layin da ake so su tsaya, daga nan kuma sai a kira su.