✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Wasu daga cikin ’yan kwallon Eaglets sun fi shekara 17 -Jaridar Meziko

Wata jarida da ake wallafawa a kasar Meziko wacce ba a ambaci sunanta ba , ta nuna da yawa daga cikin ’yan kwallon Najeriya da…

Wata jarida da ake wallafawa a kasar Meziko wacce ba a ambaci sunanta ba , ta nuna da yawa daga cikin ’yan kwallon Najeriya da ke fafatawa a gasar cin kofin duniya na matasa (U-17) suna wuce shekara 17. 

Da karfe 12 na dare, watau wayewar garin yau Juma’a ne dai Najeriya ta fafata da Meziko a wasan kusa da na karshe (Semi-Fainal) na gasar cin kofin duniya na matasa (U-17) da yanzu haka ke gudana a Chile.
Kafar sadarwa ta Sahara Reporters ce ta kalato wannan labarin, inda ta nuna jaridar ta koka ne a kan yadda Najeriya take amfani da karti majiya karfi a matsayin matasa ’yan kasa da shekara 17 (U-17) musamman a gasannin matasa daban-daban da kasar ke halarta
Najeriya ce dai ke kan gaba wajen yawan lashe kofuna a gasar, inda kawo yanzu ta lashe har sau hudu a shekaru daban-daban.
Rahotanni sun nuna watakila jaridar ta yi amfani da sharhin da tsohon dan kwallon Super Eagles Adokiye Amiesimaka ya taba yi ne a jaridar Punch a shekarar 2009 bayan ya nuna daya daga cikin ’yan kwallon Eaglets (a wancan lokaci) mai suna Fortune Chukwudi shekarunsa sun kai 25. Kocin ya ce a lokacin da yake shugabanci a kulob din Sharks na Fatakwal ya taba tara matasa ’yan kasa da shekara 20 inda ya horar da su kuma dan kwallon yana daga cikin wadanda ya ba su horo. Ya ce hakan ta faru ne a tsakanin shekarar 2002 zuwa 2003 amma bayan shekaru bakwai watau a shekarar 2009 sai ya ga an kira dan kwallon a kungiyar kwallon kafa ta ’yan kasa da shekara (17) kuma da shi aka tafi gasar cin kofin duniya. Ya ce idan har dan kwallon yana da shekara 18 a shekaru bakwai da suka wuce, to ya aka yi shekarunsa na haihuwa suka koma 17?
Ana ganin wannan ne dalilin da ya sa wata jarida a Meziko take tababar shekarun wasu daga cikin ’yan kwallon Eaglets da yanzu haka suke fafatawa a gasar cin kofin duniya na matsa da ke gudana a Chile.