✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Wasu daga cikin manufofin Aikin Hajji

Bayan kammala azumin watan Ramadan wani muhimmin rukunin addini na gaba da ke kan Musulmi mai iko shi ne aikin Hajji. Daga yanzu za mu…

Bayan kammala azumin watan Ramadan wani muhimmin rukunin addini na gaba da ke kan Musulmi mai iko shi ne aikin Hajji. Daga yanzu za mu fara kawo rubuce-rubuce kan wannan maudu’i domin nusar da maniyyata da sauran makaranta ta yadda za a samu a yi aikin Hajji karbabbe. Allah Ya sa duk ayyukan ibada da muke yi muna yi ne domin neman yardarSa kuma Ya ba mu lada a kai:

Na Khalid Bin Salamah
Fassarar Imam DSP Ahmad Adam Kutubi

Godiya ta tabbata ga Allah Wanda Ya girmama waliyyanSa da ilimi mai amfani da aiki nagari, sai Ya sanya tsoronSa da komawa zuwa gare Shi daga cikin amfanin iiiminsu, Ya daukaka wadansu mutane da wannan ilimin, Ya sanya su mafiya daukakar mutane a matsayi, kuma Ya cika wasu zukata da shi sai ta so shi, kuma ta dauku ga gamuwa da Shi, kuma Ya shagaitar da wasu gabbai da shi sai ta tsawaita tsayuwa a gaba gare Shi.
Tsira da aminci su tabbata a bisa mafificin wanda ya san Ubangijinsa, sai ya shagala da ambatonsa ga barin ambaton waninSa, kuma ya tsarkake masa bautarsa da sallarsa da rayuwarsa da mutuwarsa, har Ubangijinsa Ya zabe shi, Ya so shi, Ya yarda da shi kuma Ya sanya managarta daga bayinSa suka yarda da shi.
Ya Ubangijinmu hakika ilimi gaba dayansa a hannunKa yake, Ka azurta mu da mafi soyuwarsa gare Ka, kuma Ka daukaka matsayinmu a wajenKa da shi, ya Ubangijinmu! Ka tsare ayyukanmu da shi, kuma Ka gafarta zunubanmu da shi, kuma Ka yalwata kirazanmu da shi, kuma Ka sanya shi tsarkakke ne saboda zatinKa Mai girma. Ya Ubangijinmu! Hakika muna rokonKa dacewa da yin daidai ga abin da Kake so kuma Kake yarda da shi, cikin niyyoyi da maganganunmu da ayyukanmu.
Bayan haka: Ya kai dan uwa Musulmi! Ya dan uwana mahajjaci! Babu abu mafi kyau kamar matsayin mika wuya ga Ubangijin talikai, domin Shi ne alamar muminai, idan kuma an kara wa bawa da matsayi na sani a kan na mika wuya, sai ya kara kusanci zuwa Ubangijin talikai Mai tsarki da daukaka, ya Allah Ubangijinmu! Ka kara mana mika wuya da sani da aiki, kuma Ka karba mana da rahamarKa, ya Mai bayyana soyayyarSa! Hakika Kai ne Mawadaci Mai karamci.
Ya dan uwana Alhaji! Abu ne mai kyau ka aikata ayyukan Hajji ko da kuwa ba ka san saboda me kake aikata su ba, ya ishe ka saninka da cewa su bauta ne ga Allah Mabuwayi Mai daukaka, wannan kuwa shi ne abin da mika wuya ga Ubangijin talikai da cikakkiyar bauta gare Shi ke nema.
Amma mafi kyau daga wannan shi ne yayin da kake na ci ga Allah Ya kara maka sani, sai Ya amsa maka Ya yi maka budi, ka san hikimar wasu daga cikin ayyukan Hajji. Allah Madaukakin Sarki Ya ce: “Kuma wadanda suka yi kokari wajen neman yardarMu, lallai za Mu shiryar da su zuwa hanyoyinMu, kuma hakika Allah Yana tare da masu kyautatawa (Ankabuti). Don haka lallai abu ne mai kyau matuka mu san, cewa don me Makka ta kasance a wani kwari ba mai shuka ba, kuma ba ta kasance a wani kwari mai shuka ba da dazuzzuka da koramu, wadanda za su sa Alhaji ko mai Umara ya ji dadi a mafi soyuwar wurare ga Allah?
Kuma saboda me ya kasance daga kebance-kebancen Annabi (SA.W) cewa duga-dugansa da jikinsa ba su taba kasarArafa ba a cikin aikin Hajjin Ban-Kwana?
Kuma saboda me maza da mata ke cakuduwa ta fuskar matsatsi mai tsananta cikin dawafi da majanjifa a wani wuri tsukakke, sabanin al’adar shari’a mai hikima cikin ragowar ibadu, kuma alhali Allah Mai iko ne a bisa yalwatawa a gare su?
Kuma me ya sa yayin da muke komowa daga Arafa dole ne sai mun kwana a Muzdaiifa, tare da cewa Mina tana kusa da mu, kuma shimfidunmu da kayayyakinmu suna cikinta?
Da wasunsu daga hikimomi manya a cikin ayyukan Hajji da Umara.
Mu ba ma shakka cewa dukkan ayyukan Hajji suna da hikimomi masu girma da manufofi wadanda sai an yi zurfin tunani kafin a gano su, wanda ya san su ya san su, wanda kuma ya jahilce su ya jahilce su.
Wannnan kuwa shi ne abin da na yi nufin in fito da shi kuma in daddale shi, kuma ina janyo hankulan bayi zuwa gare shi cikin wadannan sadarori ’yan kadan, ina mai neman taimakon Allah Mai buwaya da daukaka, kuma ina mai neman agaji daga gare Shi. Fatarmu Ubangijinmu Ya yi gafara a gare mu kuma Ya jikanmu kuma Ya shiryar da mu zuwa tafarkinSa madaidaici.
Tare da la’akari da cewa ni a wadannan ’yan sadarori ban ba da kulawa da hukuncin Fikihu ba, domin wannan lamari yana da wuraren da ake samunsa wadanda malamai suka rubuta cikin tittattafan hukunce-hukunce. Sai dai ni zan mai da hankali ne ga wasu sassan manufofi masu girma wadanda da yawa daga alhazai suka rafkana ga barinsu da kuma yawa-yawan wadanda suka yi rubutu game da aikin Hajji. Ina mai aiki cikin haka da fadin Annabi (SAW): “Da yawa mutum zai dauki ilimin shari’a ya kai wa wanda ya fishi fahimtarsa.” Abu Dawud ne ya rawaito shi (3660) kuma Albani ya inganta shi.
Ina mai neman shawara cikin hakan daga wanda ya fi ni iko bisa fito da wadannan manufofi ta hanya mafi girma kuma mafi bayyana kuma mafi gamewa, kuma duk abin da ya kasance cikinsa na daidai to daga Allah ne Shi kadai, abin da kuma ya kasance cikinsa na kuskure to daga gare ni ne da kuma Shaidan.
Alkin Hajji:
Allah Madaukakin Sarki Ya ce “Kuma ku cika Hajji da Umara saboda Allah” (AI-Bakarah). Ita wannan cikawar kashi uku ce:
Tafarko: Cika aikin Hajji dangane da lokaci.
Ta biyu: Cika aikin Hajji dangane da wuri.
Ta uku: Cika aikin Hajji dangane da siffa.
Game da bayanin haka muna cewa:
Da farko: Cika shi dangane da lokaci: shi ne aikin Hajji ya faru a lokacin da Allah Mai tsarki da daukaka Ya shar’anta shi, yadda ba za mu gaggauta shi ko mu jinkirta shi daga lokacinsa ba.
Don haka kowace ibada a cikin aikin Hajji da aka kebe ta ne da wani lokaci iyakantacce; to wannan sanya lokacin yana da manufarsa wadda ba za ta taba tabbatuwa ba sai da shi, don haka wanda ya yi sakaci cikin wani lokaci da Allah Ta’ala Ya sanya shi, to hakika ya yi sakaci cikin cikata wadannan manufofi. Allah Ta’ala Ya ce: “Aikin Hajji dai watanni ne sanannu…” (AI-Bakarah).
Kuma Allah Ta’ala Ya ce: “Kuma ku ambaci Allah a cikin kwanaki sanannu.” (AI-Bakarah).
Don haka ne muke cewa ga misali: Duk wanda gaggawa ta debe shi sai bai kwana a Muzdalifah ba, ko ya fita daga cikinta kafin tsakiyar dare, haka nan wanda ya yi jifa kafin zawalin rana a ranar 12, to duk wannan yana kaiwa zuwa saba wa manufofin aikin Hajjin ko (ya jawo) tawayarta.
Na Biyu: Cikata Hajji ta bangaren wuri: Wanda shi ne a aiwatar da ibadun da Allah Ya shar’anta su a cikin Hajji a wurarensu da Allah Mai tsarki da daukaka Ya yi nufinsu. Don haka kowane bigire yana da manufofinsa wadanda ba sa tabbata sai a wajen, don haka duk wanda ya yi sakaci a cikin wani wuri na ibada, to hakika ya yi sakaci cikin cikata manufofin wannan ibada. Imam DSP Ahmad Adam Kutubi, 08036095723