’Yan sanda a Jihar Jigawa sun cafke wasu mutum biyu da ake zargi da satar shanu a Karamar Hukumar Garki ta Jihar.
Kakakin ’yan sandan jihar, ASP Lawan Shiisu ne ya shaida wa Kamfanin Dillacin Labaran Najeriya (NAN) hakan a Dutse, babban birnin jihar a ranar Litinin.
- Rayuwar Zawarawa ’Yan Kannywood Sai Hakuri -Mansurah Isah
- Najeriya A Yau: Sakacin gwamnati ne silar kai hari a makarantu A 2021
Shiisu ya ce an cafke wadanda ake zargin ne bayan wani mutum mai suna Nasiru Magaji ya shigar da kara cewa wasu mutane sun haura masa gida da misalin karfe 2:30 na dare, a ranar 14 ga watan Disamba suka sace masa shanu.
Ya ce bayan samun rahoton faruwar lamarin, aka tashi ’yan sanda inda suka shiga bincike har suka gano shanun a kasuwar garin Wudil da ke Jihar Kano.
Kakakin ya ce wadanda ake zargin masu shekara 30 a duniya, sun fito ne daga kauyen Jaya da Daware, duk a Karamar Hukumar Garki ta jihar, an same su da hannu a satar shanun.
A cewarsa, wasu mutum biyu kuma daga kauyukan Jaya da Badage a kananan hukumomin Garki da Ringim sun tsere amma ana binciked don gano inda suka shiga.
Shiisu ya ce wadanda ake zargin za a mika su zuwa kotu da zarar an kammala bincike, sannan ragowar biyun ana ci gaba da binciken don cafke su.