Firayiminista ya karba ya karanta duk abin da yake rubuce a jikin Chekue din gaba da baya har da sa hannu, sai ya miko wa Maitama Sule Chekue din ya ce da shi “ka mayar musu, ba ma bukata”. Nan-da-nan Maitama Sule ya samu jirgin sama ya mayar musu ya ce: “Gwamnati ba ta bukatar wannan kudin”. Muhammadu Buhari ya ce: “me ya sa Maitama Sule a lokacin bai ce, su yago masa Fam Miliyan daya ba? Tun da lokacin yana matashi daidai bukatar kudi, sai yanzu da ya tsufa ba ya bukatar kudi zai nemi kwangila irin wannan? Da na dawo na gaya wa danmasani, sai ya fara yake yana cewa: “lokacin ba shi da wannan hikimar kamar yadda yake cewa (I was a stupid young Minister then)”.
Allahu Akbar, halin mutum jarinsa! Maitama Sule ya taba gaya mini lokacin da ya tsaya takarar Shugaban kasa tare da Shagari a 1979 sai da Marigayi Shugaban kasar Libya (Mu’ammar Gaddafi) ya yi masa tayin taimakon kudi masu yawa, amma ya ki karba, da na tambaye shi me ya sa ya ki karba sai ya ce da ni “yana tsoron abin da zai biyo baya, idan ya ci zaben ya zama Shugaban kasa, Gaddafi ya zo da wata bukata, wadda ba ta dace da bukatar ‘yan Najeriya ba zai shiga matsala”. Haka wani matashin dan kasuwa da ya zo masa da alkawarin taimakon kudi don ya yi kamfen, shi ma dai ya ce ba ya bukata, domin dalilinsa: “tsoro yake ji ko yana cikin masu safarar cocain ne”. Ni da shi ya gaya mini wadannan maganganun. Saboda haka daga baya da sojoji suka nemi ya zo ya yi takarar Shugaban kasa (a 1990s), sai na tuna masa ba shi da kudi, ba shi da rijiyar mai, ko Gidan Mai ba shi da shi kowa ya sani, saboda haka yaudararsa kawai suke yi. Dama ni na gama fahimtar cewa Shugaban kasar wancan lokacin cikakken mayaudari ne, kuma haka ta tabbata.
Duk da irin wadannan manya-manya damarmaki da suke giftawa ta gaban Marigayi Yusuf Maitama Sule, amma yake kawar da kai saboda kana’a, sai ka ga ‘yar kankanuwar bukata ta tayar masa da hankali. Misali akwai lokacin da direbansa (Daniga) ya zo gidana sau uku a rana, akan lallai danmasani yana so in kai masa kudi, lokacin ba ni da wannan kudin a hannu, sai na rubuta masa Chekue na ranar Litinin ya kai masa, danmasani bai jira Litinin din ba, saiya jinginar da Chekue din aka ba shi wasu kudin ya raba wa mutane saboda karamci irin nasa. Idan ya bukaci wani abu na ga zai tambayi wanda nake ganin bai kamata ba, nakan tuna masa baya sai ya ce “to ni in je in samo masa, idan abin da bai fi karfina ba ne, sai in yi sannan a zauna lafiya, har Allah Ya sa abubuwa suka fara yi masa daidai.
Lokacin da IBB ya nuna masa zai taimaka ya tsaya takarar Shugaban Kasa ya yarda. Da ya gaya min, na ce yaudararka zai yi, idan yana so ya taimake ka ya ba ka Rijiyar Mai ko Lifting na Mai, tun da ya bai wa wasu da ba su kai ka ba, ya san ka yi Ministan Mai tsawon shekaru kusan bakwai (7), ko Gidan Mai ba ka mallaka ba. Sai aka musanya shi da Bashir Othman Tofa, duk a karshe aka ji kunya baki daya. Sai ya fara bude musu wuta, har ya so in dinga taya shi. Abin da yake wahalar da ni, sau da yawa zan fahimci wasu abubuwa da illolinsu,in fada wa duniya kowa ya ji, amma mutanen da suka kamata su gane su dauki matakin gyara, ba sa ko damuwa sai abu ya zama alakakai sannan a yi fargar Jaji.
Alhamdulillahi, duk da kasancewar danmasanin Kano, bai mallaki Masana’anta ko Kamfani ko gona ko hannun jari ko ajiyar banki ba, babu wanda zai ci mana mutunci a kansa, Allah Ya sa shi, ba barawo ba ne, ba mugu ba ne, sai karamci da bayin Allah na kwarai suke nuna mana tun yana da rai, har Allah Ya karbi rayuwarsa cikin rufin asiri. Allah Ya sa can ta fi nan a gare shi.
Allah Ya saka wa kowa da mafificin alkhairi a kan irin gudunmawar da kowa ya bayar a al’amuran rayuwar danmasani har izuwa rasuwarsa. Allah Ya hada mu a Gidan Rahama (Jannatul Firdausi), tare da duk magabatanmu da iyalanmu da zuriyarmu da majibanta lamuranmu, amin.
Darussan da rayuwar Yusuf Maitama Sule, ba shi da riko, idan ya fahimci ya bata wa wani, zai ta neman sa ya ba shi hakuri. Kamar yadda ta faru a kaina, mukan yi mahawara (wani lokacin mai zafi) a kan in hana shi wasu abubuwan da nake ganin ba su dace ya yi ba, ga shi da yawan wasa da barkwanci, sai ya manta ni kaninsa ne ba abokin wasansa ba, a kan haka na koka masa har na yi fushi, na daina zuwa wajensa, har ya fahimci kuskurensa, ya damu kwarai, ya sa wani kaninsa (wanda ni wa ne a gare ni), da Mahaifinsa da Mahaifiyar Maitama Sule da Mahaifiyata duk Uwarsu daya Ubansu daya, yayi ta nemana a waya yana gaya min danmasani yana nemana, ya damu in je mu hadu, har ta kai danmasani ya sanar da Mukhtari (babban dansa a maza), muna kan hanyar dawowa daga Maiduguri daga daurin auren wani jikan danmasanin mun tsaya a Masallaci za mu yi Sallah, sai Mukhtari ya ce da ni “Danmasani har rashin lafiya ya yi, ya damu in je mu hadu”. Wannan maganar har a wurin Alhaji Sani Zangon Daura (danmasanin Daura) sai da na ji ta. Ranar da na je wajen Maitama Sule muka kebe da shi, sai na ce masa “duk cikin zuri’armu bangaren uwa da na uba, ina ga babu wanda ya yi mawafakar da na yi, don na ga duk kakannina hudu, sun sanni na sansu, iyayena biyu uwa da uba Allah Ya hada mu tafiya lokaci guda zuwa Aikin Hajji (a lokacin da aurena har da (‘ya ‘ya) mun je Ka’abah da masallacin Annabi (S.A.W) da Arfa duk sun yi mini addu’a. Ban taba jin wani daga cikin kakannina ko iyayena ko wani a cikin ‘yan uwansu ya kyare ni ba, sai kai ne za ka hantare ni a kan na fadi gaskiya?” Take ya ba ni hakuri. Haka danmasani yake.
danmasanin Kano, Alhaji Yusuf Maitama Sule, ya rasu ranar Litinin 3 ga watan Yuli, 2017 (3/7/2017) yana da shekaru 88, ya bar matarsa daya da ‘ya ‘ya 10- maza hudu, mata shida. Da ma ‘ya ‘ya 13 ya haifa a rayuwarsa, amma uku (3) sun riga shi rasuwa. Ya kuma bar jikoki masu yawa. Allah Ya jikansa, Ya albarkaci bayansa, amin.
Abin da na kara koya a rayuwar danmasani shi ne, ba ya shakkar fada wa kowa gaskiya (komai matsayinsa), ga shi da fikira da hangen nesa da baiwar magana da iya isar da sako cikin hikima. Shi ya sa Shugaba Obasanjo ya ce: “idan har ba ka son a gamsar da kai a kan wani abu, to kar ka saurari Maitama Sule (if you don’t want be conbinced, don’t listen to Maitama)” – Ma’ana, idan har Marigayi danmasanin Kano ya zo da wani bayani, da wahala a ce bai gamsar da kai ba.
Da ya je jinya London, kusan duk abin da kowa ya ba shi na gudunmawa, sai da ya zayyana mini abin da kowa ya ba shi, daga wanda ya ba shi Dala dubu daya zuwa Fam Dubu Biyar da sauransu. Haka wadanda suka ziyarce shi, su ma duk ya fada mini, har yake gaya mini Marigayi Galadiman Kano (Alhaji Tijjani Hashim) sun je duba shi tare da dan Iya Ado Sunusi, a lokacin shi ma Galadima Tijjani Hashim yana fama da ciwon kafa, don a kujerar masu jinya ake tura shi. Ina addu’a ga duk wanda suka ci gaba da taimaka masa (har Allah Ya karbi rayuwarsa), Allah Ya saka wa kowa da mafificin alkhairi, Allah Ya amfani bayansa, Ya albarkaci wadanda ya bari, amin. Wasu maganganun da ya gaya min dab da rasuwarsa (kimanin wata hudu kafin rasuwarsa), sai yanzu nake ganin kamar Wasiyya ce.
Alhaji Abdulkarim Daiyabu, Shugaban Rundunar Adalci ta Najeriya (Mobement for Justice In Nigeria – MOJIN) Tsohon Shugaban Kungiyar ‘Yan Kasuwa da masu Masana’antu, Harkar Ma’adanai da Ayyukan Gona (Kano Chamber of Commerce, Industry, Mines and Agriculture -KACCIMA) Tsohon Shugaban Jam’iyyar Alliance for Democracy (AD) na Kasa. 08023106666 ; 08060116666