A ranar Litinin daya ga Fabrairun bara, da Asuba ina shirye-shiryan tafiya, sai na ji ana buga kofar gida ana kirana. Jin ana kiran sunana da yadda na bar jikin mahaifina cikin dare ranar Lahadi, sai jikina ya ba ni akwai matsala.
Ina fitowa falo, sai na duba wayata na ga kira biyar. Nan na ce ‘Inna lillahi wa inna ilaihirajiuna.’ Na san labarin da za a kawo min. Bude kofar ke da wuya na ga Hamza da Umar suka ce min baba fa ya rasu.
- Muhimman batutuwan da za su mamaye taron Shugabannin Afirka a Habasha
- ’Yan Mali na murnar fatattakar jakadan Faransa daga kasarsu
Ban ce musu komai ba, sai na dawo gida na tashe matata, na fada mata abin da ake ciki, ta tashi a firgice ta nufa gidan.
Na nemi ruwa na yi alwala, na yi Sallah raka’a biyu na nema wa mahaifina gafarar Allah.
Da na kammala, sai na fito na tafi masallaci domin Sallar Asuba. Da aka sallame sai ladan ya tashi zai yi sanarwa. Na ji ras: domin na dade ina jin irin wannan sanarwar, kuma na dade ina tunanin yaya zan ji idan sanarwar nan ta zo kaina. Ai kuwa haka ya ce: Allah Ya yi wa Malam Muhammad Ango rasuwa.
Mahaifina Malam Muhammad Ango Kanzaure, mutum ne da a duniya ban taba ganin irinsa ba. Ya taso cikin rayuwa mai kyau da saukin kai da hidimar addini da iyali da ’yan uwa.
Na taso da son karatun Kur’ani ne bayan na taso ina ganinsa kullum yana karanta Kur’ani a gida. Sannan ko me muke yi a gida, da zarar karfe 8:30 ta yi za mu yi shiru, domin zai fara sauraron wa’azin ‘Rabin sa’a’ na marigayi Sheikh Abubakar Mahmud Gumi.
Marigayi mahaifina tamkar ruwa ne, wanda ba ya da abokin gaba. Mutane da dama a dangi da wadansu a kasuwa sukan takale shi, amma kamar bai ma san suna yi ba. Kullum ba ruwansa, burinsa kawai ibada da neman kusanci ga Allah da hidimar iyalinsa.
Na taso kullum idan zan ga mahaifina ido-da-ido, ba ma rabuwa sai ya ba ni kudi. Gatar nan ta sa ina karami duk lokacin da aka yi tuwo sai in ce ba zan ci ba, sai ya ba ni kudi ya ce in sayi wani abu in ci. Haka na taso kuma har yanzu ba na cin tuwon.
Sannan duk da cewa bai yi karatun boko ba, da ina jami’a, kullum sai ya ba ni kudi har na kammala karatuna. Kuma na tuna sau daya ya taba kai min mari saboda an aike ni na dade ban dawo ba. Amma bayan nan, ko daga murya bai cika yi ba.
Idan ka ji ya daga murya, to karatun Kur’ani yake yi. Shi ya koyar da ni karatun Kawa’idi da Ahlari. Idan ya yi Sallar Asuba, a masallaci yake zama ya yi karatun Kur’ani har safiya, sannan ya tafi kasuwa, sai bayan Sallar Isha ya dawo.
Da ya dawo gida zai shiga bai fitowa idan ba da wani dalili babba ba. Sannan a daren ma, daga Sallah sai karatun Kur’ani kafin ya yi barci.
Lokacin da rashin lafiyarsa ta yi tsanani, ko magana ba ya iya yi, amma da zarar lokacin Sallah ya yi, zai ce a daga shi zai je masallaci har Sallar Asuba ma sai ya ce a kai shi masallaci. Ba na mantawa ya taba yi min kukan cewa masu jinyarsa sun hana shi zuwa masallaci. Haka da ya samu dan sauki, sai ka gan shi da Kur’ani.
Madalla da uba nagari wanda ya yi kokarin kwatanta halayen kirki. Kowa a haka ya san shi, kuma a haka ya rasu. Lokacin yana raye mutane sukan tambaye ni, shin babanku yana magana kuwa? Nakan amsa musu da cewa yana magana, amma sai magana mai muhimmanci.
Ina fata kana kwance cikin rahamar Allah kwanciyar hankali da natsuwa a kabarinka. Lallai ka tafi ka bar duniyar nanmai cike da yamutsi da zunubai da kalubale masu yawa, sannan ka tafi ne a lokacin da na fi bukatarka. Ina da yakinin kana cikin salihan bayi.
Ka tuna lokacin da ina karami, kullum ko na ci abinci idan ka dawo sai ka rage min? To ni ma haka na fara wa jikarka Maryam (Ilham). Sannan ka tuna lokacin da ina karami nake zuwa bakin titi ina kuka ina nemanka saboda ba ka dawo daga kasuwa ba? To ni ma yanzu haka jikarka takan ce a kira mata babanta a waya.
Zumuncin da ka rika cewa mu sadar, muna kwatantawa bakin kokarinmu. Ina autarka a bangaren mata, Khadija. Wata mai zuwa insha Allahu za ta yi aure. Sai dai kash! Za ta yi aure a lokacin da ba ka tare da mu, amma wakilinka da tun kana raye kake turawa a al’amari irin wannan, shi ne zai wakilce ka.
Dan autanka baki daya kuma Ibrahim yana nan yana karatu, kuma yadda ka fada kake so a game da shi, insha Allah za mu cika. Mahaifiyarmu muna nan muna ci gaba da lura da ita tamkar kana raye.
A karshe akwai abin da ban taba fada maka ba, amma na fada wa wadansu. Burina a duniya shi ne in gina maka gida in saya maka mota, in dauka maka direba ya riga kai ka duk inda za ka je ya dawo da kai.
Amma kash! Sai mutuwa ta min yankar kauna. Sai dai ina da yakinin kana gidan da ya fi gidan da na yi da burin in gina maka girma da alfarma. Sannan kana tare da ayyyukan alheri da ka gabatar a duniya suna taya ka zama cikin kwanciyar hankali da natsuwa da jin dadi.
Allah Ya kara maka kwanciyar hankali da haske da natsuwa a kabarinka. Allah Ya sada mu da kai a Aljanna.
Daga danka, Isiyaku Muhammed Ango.
07036223691