✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Wasan Sada Zumunta: Najeriya ta doke Laberiya da ci 2-1

A ranar Talatar da ta wuce ce kungiyar kwallon kafa ta Super Eagles ta Najeriya ta lallasa takwararta ta Laberiya ta ci 2-1 a wani…

A ranar Talatar da ta wuce ce kungiyar kwallon kafa ta Super Eagles ta Najeriya ta lallasa takwararta ta Laberiya ta ci 2-1 a wani wasan sada zumunta da aka yi a kasar Laberiya.

Shugaban kasar Laberiya, Mista George Weah ne ya shirya wasan sada zumuntar don yin ban-kwana da riga Mai lamba 14 da ya yi amfani da ita a lokacin da yake buga wa kasar kwallo.

Henry Onyekuru wanda aka sake gayyata zuwa kungiyar Super Eagles ne ya zura kwallon farko a raga a daidai minti na 11 da fara wasa bayan John Ogu ya tura masa wata kwallo.

A daidai minti na 33 Simeon Nwankwo ya jefa kwallo ta biyu bayan Etebo ya yi bugun kusurwa.

A daidai minti na 89 ne dan kwallon Laberiya Palsama ya zura kwallo a ragar Najeriya da hakan ya sa aka tashi wasan 2-1.

Idan za a tuna, a farkon  bana ne George Weah ya zama Shugaban kasar Laberiya, al’amarin da ya sa ya zama dan kwallo na farko da ya zama Shugaban kasa a duk fadin duniya.