Hukumar kwallon kafa ta Nahiyar Afrika (CAF) ta ce ba za a bar ’yar kallo da ’yan jarida su shiga filin wasa a lokacin wasan neman gurbin Gasar Cin Kofin Afirka ba.
Shugaban CAF Bola Oyeyode ya shaida wa manema labarai cewa babu wani dan jarida ko dan kallo da za a kyale ya shiga wasan neman gurbi da za ayi tsakanin Najeriya da Saliyo.
- An cafke boka zai kwakule idanun jariri a Kano
- ’Yan Najeriya miliyan 14.3 ne ke shan miyagun kwayoyi —NDLEA
- An yi garkuwa dan uwan Mataimakin Gwamnan Edo
Oyeyode ya ce hukumar ta ce ta dauki matakin ne domin kaucewa yada cutar coronavirus.
Ya ce ko za a bar wasu ’yan jarida su shiga, masu magana da yawun kungiyoyin biyu da gidajen talabijin da aka amince da su ne kadai za su iya daukar hotuna su watsa ko magana da ’yan jarida.
Ranar Juma’a 13 ga watan Nuwamba 2020 ce kungiyar kwallon kafa ta Najeriya, Super Eagles da takwarar ta kasar Saliyo za su kece raini a wasan neman gurbin shiga gasar.