✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Wasan Masar da Najeriya: Dalung ya ba ’yan Najeriya hakuri

Ministan Wasanni Barista Solomon Dalung a shekaranjiya Laraba ne ya fito a kafar sadarwarsa ta Twitter ya ba ’yan Najeriya hakuri a bisa rashin hayewar…

Ministan Wasanni Barista Solomon Dalung a shekaranjiya Laraba ne ya fito a kafar sadarwarsa ta Twitter ya ba ’yan Najeriya hakuri a bisa rashin hayewar Super Eagles gasar cin kofin Afirka bayan Masar ta lallasa Najeriya da ci 1-0 a ranar Talatar da ta wuce.
Wannan ci da Masar ta yi wa Najeriya ya nuna ba za ta samu damar zuwa gasar cin kofin Afirka da zai gudana a badi a Gabon ba ko da ta samu nasara a sauran wasa daya da ya rage mata.
Jim kadan bayan an tashi wasan ne ’yan Najeriya da dama suka nuna bacin ransu a game da yadda Masar ta fitar da Najeriya.  Kuma wannan shi ne karo na biyu a jere da Najeriya ba za ta halarci gasar cin kofin Afirka ba.  Super Eagles ba ta halarci gasar cin kofin Afirka da ya gudana a Ekuatorial Guinea ba a shekarar 2015 yanzu kuma ba za ta halarci wanda za a yi a Gabon a shekarar 2017 ba.
Sai dai Ministan ya dora laifin rashin hayewar Najeriya gasar ce akan Shugabannin Hukumar kwallon kafa ta kasa (NFF). Ya ce bisa yadda shugabannin suka mayar da hankali wajen yin fada a bisa shugabancin hukumar ne ya janyo wa Super Eagles matsala, kuma wannan ya zama abin takaici.
“Yadda shugabannin hukumar NFF suke ta takaddama a kan sha’anin shugabanci ne ta sa abin ya shafi kungiyar Super Eagles, don haka babu wanda na dora wa laifi face hukumar NFF a kan wannan abin bakin cikin da ya samu Super Eagles”, inji shi.
Shi ma kocin kungiyar na riko Samson Siasia ya ce babban dalilin da ya sa ba su samu nasarar hayewa gasar cin kofin Afirka a wannan karo ba shi ne ganin yadda ya gaji kungiyar daga tsohon koci Sunday Oliseh ne bayan ya jeta ta cikin mawuyacin hali.  Kocin ya ce duk da haka ’yan kwallon sun yi kokari sai dai rashin sa’a ce kurum ta janyo haka musamman idan aka yi la’akari da wasan da kungiyar ta yi a Kaduna da Masar, bayan Masar ta farke cin da aka yi mata ana saura minti biyu kacal a tashi daga wasan.