Akalla mutum hudu aka kashe sannan aka kone gidaje da dama a wani rikici tsakanin Fulani makiyaya da wasu matasan kabilar Irigwe a kauyukan Karamar Hukumar Bassa ta Jihar Filato.
Kakakin rundunar ’yan sandan Jihar, ASP Ubah Gabriel, wanda ya tabbatar da faruwar lamarin, ya ce gidaje 50 ne abin ya shafa.
- Ba dan kungiyarmu Hisbah ta kama ba a Kano —PSN
- Za a yi wa yara miliyan 1.7 rigakafin shan-inna a Jigawa
Ya ce, “A ranar Asabar 31 ga watan Yulin 2021, rundunar ta samu rahoton cewa rikici ya hautsine tsakanin ’yan bindiga da ake zargi Fulani makiyaya ne da matasan kabilar Irigwe a Jebbu Miango, Karamar Hukumar Bassa ta Jihar Filato.
“Babban abin takaici shi ne yadda aka kone gidaje 50 kari a kan harbe wasu mutum hudu ‘’yan gida daya.
“Bayan samun rahoton, nan take aka tura wata tawagar jami’anmu zuwa wurin domin kwantar da tarzoma.
“Kwamishinan ’yan sanda, CP Edward Egbuka, tare da wasu manyan jami’an ’yan sandan sun ziyarci wurin kuma sun ba da umurnin gudanar da bincike don gano wadanda suka aikata wannan danyen aiki.
“Tuni dai tarzoma ta lafa kuma al’amura sun daidaita a yankin ya zuwa yanzu, ”in ji shi.
Bayanai sun ce fiye da mutane 10 sun jikkata yayin arangamar inda dukkan bangarorin biyu da abin ya shafa ke zargin juna da haddasa rikicin.
Wakilinmu ya ruwaito cewa, rikicin ya fara aukuwa ne tun a ranar Alhamis ta makon jiya har ya zuwa daren Asabar.
Shugaban Kungiyar Ci gaban Fulani ta Gan Fulani (GAFDAN), Garba Abdullahi ya ce, “Fiye da makiyaya 10 sun ji rauni kuma an kai su asibiti inda suke karbar magani.
Danjuma Autta, Sakatare-Janar na Kabilar Irigwe, ya shaida wa wakilinmu cewar an gano gawar hudu bayan barkewar rikicin, inda ya zargi gwamnati da rashin yin katabus kafin rikicin ya kai ga halin da ake ciki.
Ya ce, “Akwai sakaci daga bangaren gwamnati da ya sa rikicin ya kai haka, lamarin da ya zama tamkar yaki.
“An sa ran cewa gwamnati za ta yi wani abu kafin munanar lamarin. Bai kamata ta bari rashin fahimta ya koma rikici ba.
“Muna bukatar zaman lafiya, ya kamata gwamnati ta tashi tsaye wajen sauke nauyin da ke wuyanta na kare rayuka da dukiyoyin al’umma don kowane rai na da matukar mahimmanci,” a cewar Autta.