Rundunar ’Yan Sandan Jihar Legas, ta tabbatar da rasuwar wani mutum mai shekara 58 a duniya, sakamakon shafe kwanaki 19 yana azumin ba tare da ya sha ruwa ba.
Kakakin rundunar ’yan sandan, SP Benjamin Hundeyin ne, ya bayyana hakan a ranar Talata.
- Gwamnan Filato ya dakatar da Kwamishinoninsa 2
- An tsare mai kemis da ya yi wa yarinya fyaɗe, ta rasu a Kano
Ya ce lamarin ya faru ne a yankin Alagbado na jihar a ranar Litinin da misalin ƙarfe 6 na safe.
Ya ce ɗan uwan mamaci ne, ya kai rahoto faruwar lamarin ofishin ‘yan sanda na Alagbado a ranar Litinin cewa ɗan uwansa ya rasu sakamakon shafe kwanaki 19 yana azumi.
Hundeyin ya ce, “Babu wani abu da aka zargi ya faru da shi, ‘yan uwansa sun buƙaci a kai gawar don birne ta.” (NAN)