✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Wani mutum ya rasu sakamakon azumin kwana 19 a Legas

An ruwaito cewar mutumin ya shafe kwanaki yana azumi ba tare da ya sauke ba.

Rundunar ’Yan Sandan Jihar Legas, ta tabbatar da rasuwar wani mutum mai shekara 58 a duniya, sakamakon shafe kwanaki 19 yana azumin ba tare da ya sha ruwa ba.

Kakakin rundunar ’yan sandan, SP Benjamin Hundeyin ne, ya bayyana hakan a ranar Talata.

Ya ce lamarin ya faru ne a yankin Alagbado na jihar a ranar Litinin da misalin ƙarfe 6 na safe.

Ya ce ɗan uwan mamaci ne, ya kai rahoto faruwar lamarin ofishin ‘yan sanda na Alagbado a ranar Litinin cewa ɗan uwansa ya rasu sakamakon shafe kwanaki 19 yana azumi.

Hundeyin ya ce, “Babu wani abu da aka zargi ya faru da shi, ‘yan uwansa sun buƙaci a kai gawar don birne ta.” (NAN)