✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Wani mutum ya mutu a gasar shan burkutu a Abuja

Ya mutu ne bayan ya yi mata shan wuce ka'ida

Wani mutum ya rasa ransa a sakamakon yawan barasar da ya sha a wata gasa tsakanin shi da abokansa a Kubwa da ke yankin Babban Birnin Tarayya Abuja.

Wannan lamari ya faru ne a yankin Byzhin da ke unguwar ta Kubwa a ranar Asabar, a inda wata gasa ce mutumin da ya a sha wani adadi na kabakin barasar burkutu da ta yi ajalinsa.

Wani mazaunin unguwar mai suna Bello Yusuf, wanda kuma lamarin ya faru a idonsa ya shaida wa Aminiya cewa, mutumin sunansa Hassan, ya yi tatil ne da burkutu a wata gasa da suke yi shi da abokansa a inda ya yi sha mata sha-kundum.

“Da ganin marigayin ya yi shan da ya wuce lissafi kuma ya soma amai ba kakkautawa har ya suma, sai abokan nasa suka kai shi wani kango don ya farfado, amma sai rai ya yi halinsa,” inji Bello.

Ganin cewa ya mutu sai abokansa nasa suka gudu, suka bar gawar a nan.

“Da ma fitinannun gari ne, wandanda ba a sa su, ba a hana su,” a cewar Bello.

Wani jami’in ‘yan sanda da ke Kubwa ya tabbatar wa Aminiya faruwar lamarin.