✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Wani mutum ya mutu bayan ya kashe makwabcinsa

Wani mutum da ake zaton yana da tabin hankali ya kashe makwabcinsa tare da farfasa motar mai gidan hayar da yake ciki a unguwar Awosuru…

Wani mutum da ake zaton yana da tabin hankali ya kashe makwabcinsa tare da farfasa motar mai gidan hayar da yake ciki a unguwar Awosuru da ke birnin Osogbo, Jihar Osun.

Mazauna unguwar sun bayyana wa Aminiya cewa, mutumin ya daba wa abokin zaman nasa wuka wadda ta yi sanadiyar mutuwarsa a ranar Laraba bayan sabanin da suka samu, kafin daga baya wanda ake zargin ya yi mutuwar ban mamaki.

An ce kisan da ya yi da yanayin yadda ya fusata ya tayar da hankalin ’yan unguwar har wasu da dama suka tsere daga yankin.

’Yan unguwar sun cika da al’ajabi bayan da aka tsinci gawar wanda ake zarign a cikin gidan ba tare a sanin dalilin mutuwarsa ba.

Wani dan unguwar, Taiwo Kasali, ya ce mamacin kirki ne amma sun lura da alamun tabin hankali tattare da shi.

“Mun lura hankalinsa ba daidai yake ba, amma ban taba tsammanin abin zai kai ga haka ba.

“Ya kashe Adeleke, sa’annan kafin ya mutu, ya lalata abubuwa da dama”, inji Kasali.

Kakakin Rundunar ’Yan Sandan jihar, Yemisi Opalola ta tabbatar da faruwar lamarin.

“Mutumin ya mutu bayan ya kashe wani makwabcinsa a ranar Laraba amma ba mu san abin da ya kashe shi ba, sai dai ana kan gudanar da binciken”, inji ta.