’Yan Arewa ’yan kasuwa a garin Iwo da ke Jihar Osun sun yaba da kafuwar kasuwar Musulunci ta Mufti da ke Rukunin Gidajen Daarul Hijirah a garin Iwo.
Kasuwar wacce ita ce irinta ta farko a faɗin Nijeriya tana ci ne duk bayan kwanaki biyar.
Shaihin malamin addinin Islama, Sheikh Daood Imran Molaasan, Babban Mufti na ƙasar Yarbawa da jihohin Edo da Delta ne ya asassa kasuwar a ranar Juma’a 19 ga watan Yulin 2024 da zummar sauƙaƙa wa al’ummar yankin tsadar farashin kayan abinci da ake fama da shi a wannan lokaci, a ƙarƙashin inuwar ƙungiyar Musulmi ta Jama’at Ta’awunil Muslimin.
- An kama miji da mata kan satar buhunan shinkafa a gidan marayu
- An samu ƙaruwar sace-sace da ƙananan yaran Hausawa ke yi a Ibadan
Shahin malamin ya shaida wa Aminiya cewa, sun ɗauki wasu matakai domin samun daidaiton farashin kayan masarufi a kasuwar, ta hanyar samar da kayan abincin da suka noma suka kuma sarrafa su kai-tsaye, inda suka fara da garin rogo wanda suna da masana’antar da ke sarrafa rogon ta kuma samar da garin.
Kuma sun yi ƙoƙarin kawar da ɗabi’ar nan ta dillalai ko dillanci wanda ke ƙara hauhawar farashi, ta hanyar sadar da manoma kai-tsaye ga ’yan kasuwa.
Ya ce, a kasuwar ba a karɓar kuɗin haraji na gwamnati ko kuma na waɗanda suka kafa kasuwar, inda ake bai wa kowane ɗan kasuwa dama ya zo ya baje hajarsa ya yi kasuwanci ba tare da an karɓi ko sisin kwabo daga hannunsa ba.
Wannnan ne a cewarsa, yake basu damar ƙayyade farashin da suke so ’yan kasuwar su sayar da kayansu.
Muhammadu Bashir da ke sayar da kayan hatsi a kasuwar ya shaida wa Aminiya cewa, sun yi murna da kafuwar kasuwar duba da yadda ake kasuwanci cikin rahusa da adalci.
“Ka ga a nan suna kula da mudun da ake awo, don tabbatar da ba a tauye haƙƙin jama’a masu saye ba, kuma mu suna sauƙaƙa mana ba ma biyan kuɗin tikiti ko haraji da ake karɓa a wasu kasuwannin, kuma ba ma biyan kuɗin rumfa, wannan ne ya sa muke iya yin kasuwancin cikin rangwame kamar yadda suke buƙata; fatanmu a samu yawaitar irin wannan kasuwa a sassan Jihar Osun da ma Nijeriya baki ɗaya”, in ji shi.
Baya ga kayan hatsi, ’yan Arewar na sayar da kayan miya da kayan marmari, a yayin da kasuwar take ci gaba da karɓar baƙuncin tarin ’yan kasuwa daga sassan jihar.
Baya ga mahimman kayan abinci ana sayar da kayan amfanin yau da kullum da kayan koli da takalma da sauransu a wannan kasuwa ta Musulunci.
A cewar malamin da ya assasa kasuwar, sun kafa ta ne don bada gudunmawa ga al’umma, kuma taimakon gwamnati da mahukunta ne.
Ya ce akwai ƙalubalen da suke fuskanta, amma hakan ba zai rage masu ƙwarin gwiwa ba, kuma a yanzu suna shirin fara noma gadan-gadan a ci gaba da ƙoƙarinsu na sauƙaƙa wa al’umma da samar da wadataccen abinci.