Wani mutum mai shekaru 50 ya harbe wani ma’aikacin gidan mai saboda kin sayar masa da barasa a Kasar Jamus.
Tuni kotu a kasar ta yanke wa wani mutun hukuncin daurin rai da rai sakamakon laifin da ta tabbatar ya aikata.
- Gwagwarmayar da muka sha kafin kafa Bankin Jaiz —Hassan Usman
- Muna bukatar taimakon abinci —Pakistan
Kotun wadda ta yi zamanta a garin Bad Kreuznach ta ce, mutumin ya aikata laifin ne a garin Idar-Oberstein tun a watan Satumbar 2021.
Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya NAN ya ruwaito cewa, mutumin ya harbe ma’aikacin gidan man ne saboda ya ki sayar masa da barasa bisa dalilin rashin sanya takunkumin rufe fuska alhali ana fama da annobar da Coronavirus a lokacin.
Bayanai sun ce wannan lamari ne ya fusata mutumin da ya tafi laluben bindiga kuma ya dawo ya harbe shi da ita.
Jami’an tsaro sun ce wanda aka samu da laifin dan asalin kasar Jamus din ne, kuma ba shi da tarihin karya doka a baya.
Mutumin bayan shigarsa hannu, ya ce ya dade yana bakin cikin matsin da annobar cutar Coronavirus ta zo da shi, kuma wannan ne dalilin daukar matakin domin ya huce takaici.