Hukumar Hisbah ta Jihar Kano, ta kama wata mota maƙare da kwalaben barasa sama da 24,000 a kan titin BUK da ke Jihar.
Mataimakin Kwamanda Janar na Hukumar, Dokta Mujaheed Aminudden ne, ya bayyana haka yayin da yake tattaunawa da Aminiya a ranar Talata.
- An tsare mai kemis da ya yi wa yarinya fyaɗe, ta rasu a Kano
- Biden na hawa jirgin shekara 30, Najeriya ta yi watsi da jirgin shekara 19
Ya bayyana cewa an kama motar ne ranar Litinin da tsakar rana a daidai lokacin da ta ke ƙoƙarin shiga cikin gari.
Kazalika, ya bayyana cewa dokar hukumar Hisbah ta haramta sayarwa da shan barasa da sayar kayan maye a jihar.
Ya ce hukumar ta ƙudiri aniyar wayar wa al’umma kai game da hatsarin da ke tattare da ta’ammali da kayan maye.
Mujaheed, ya yaba wa jami’an KAROTA waɗanda suka yi ƙoƙarin tare motar kafin ta shiga cikin gari.
Ya kuma ƙara da cewa hukumar ta lashi takobin ci gaba da yaƙin da ta ke yi da masu shigo da giya cikin jihar.
Ya, kuma bayyana cewa a yanzu haka motar barasar na hedikwayar Hisbah da ke Sharada.
A cewarsa da zarar sun samu umarnin kotu za su yi ƙoƙarin lalata barasar kamar yadda suka saba.
“Direban motar ya tsere ya bar motar, don haka muka kira janwe ta kai mana motar zuwa ofis dinmu.”
Ya kuma yi kira ga al’umma da su riƙa kai rahoton duk wata mota da suke zargin tana ɗauke da kayan maye ga hukumar.