✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Wani mutum ya karbi rigakafin Coronavirus sau 87 a Jamus

Mutumin ya rika karbar rigakafi sau uku a kowace rana.

Hukumomi a Jamus sun kama wani Bajamushe da ya yi rigakafin coronavirus akalla sau 87.

Rahotanni sun ce mutumin ya rika karbar rigakafi sau uku a kowace rana a cibiyoyin yin rigakafin daban-daban na jihar Saxony da ke gabashin Jamus.

Asirin mutumin ya tonu bayan da wani malamin asibiti ya gane fuskarsa a matsayin wanda ya jima yana zuwa karbar rigakafi a wata cibiya, nan take ya kira ‘yan sanda suka zo su kama mutumin da kawo yanzu ba a bayyana sunansa ba.

Bajamushen dai ya rika gabatar wa malaman rigakafi, sabon katin shaidar rigakafi wanda ba ya nuna cewa an yi masa rigakafin Coronavirus a baya.

Da zarar an kammala yi masa sai ya yage takardar ya sake nausawa wata cibiyar rigakafin domin cimma burinsa.

Kungiyar Red Cross a Jamus na zargin mutumin da sayar wa da jama’a shaidar karbar rigakafin coronavirus 87 da ya karba.

Sai dai shi kuma bai kai ga bayyana dalilinsa na daukar wannan mataki ba kamar yadda DW ya ruwaito.