✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Wani mutum ya banka wa jirgin fasinja wuta a Ilori

Mutumin ya tsere bayan banka wa jirgin wuta.

Wani mutum ya cinna wa jirgin kasan daukar fasinja da kaya wuta a Jihar Kwara.

Lamarin wanda ya faru a ranar Laraba a Karamar Hukumar Offa, ya yi sanadin konewar biyu daga cikin tarago 15 da jirgin ke dauke da su.

Wasu majiyoyi sun shaida wa Aminiya cewa wani bata-gari ne ya cinna wa taragon jirgin kasan wuta sannan ya tsere.

Sai dai har yanzu babu wani cikakken bayani game da dalilin da ya sa mutumin ya banka wa jirgin wuta.

Da yake tabbatar da faruwar lamarin, Shugaban Hukumar Kashe Gobara ta jihar, Hakeem Adekunle, ya ce sun samu sun kashe wutar kafin ta kama sauran taragon jirgin.

A cewarsa, jirgin ya samu matsala kafin tashinsa amma an yi nasarar gyara shi kafin wani mutum da ba a san ko wane ne ba ya banka masa wuta.

“Da gangan aka cinna wa jirgin wuta. Amma mun yi nasarar kashe ta ba tare da ta kama ragowar taragon.

“Don haka ana jan hankalin mutane cewa da zarar sun ga wani abu da ya shafi gobara ko wuta, su hanzarta su sanar da hukumar kashe gobara a kan lokaci,” a cewarsa.