Wani mutum a garin Daura da ke Jihar Katsina ya kashe kan shi ta hanyar rataya saboda tsintar kansa cikin kunci na rayuwa.
Bayanai sun ce mutumin ya debe wa kansa tsammani ne saboda yunwa da fatara ce ake zargi suka yi sanadi.
- Buhari ya taya Amurka murnar cika shekara 245 da samun ’yanci
- Yaushe Jacob Zuma zai fara zaman kaso?
Aminiya ta samu rahoton cewa, mutumin wanda ba a fadi sunan shi ba, ya dade yana wannan yunkuri na kashe kan shi saboda tsananin talauci da yunwa.
Sai dai kuma wata majiyar ta ce, ana zargin mutumin yana da tabin hankali, domin ya sha fadin zai kashe kan shi.
Zuwa yanzu dai babu wani bayani a hukumance da ya tabbatar da sanadiyar mutuwar mutumin ta hanyar rataya.
Aminiya na ci gaba da bibiyar lamarin a halin yanzu domin samun cikakken rahoto.