✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Wani matashi ya kashe bakaken fata 10 a Amurka

Matashin kashe mutanen yayin da suke tsaka da sayayya a shagon sayar da kayayyaki.

Wani matashi dan shekara 18 dauke da muggan makamai, ya bindige mutane 10 a yankin Buffalo da ke New York a kasar Amurka.

Lamarin ya faru yayin da mutanen ke sayen kayan abinci a wani babban shago, harin da ya dauka kai tsaye ta dandalin sada zumunta, a cewar hukumomi, wadanda suka ce yana da nasaba da wariyar launin fata.

Matashin wanda ya ke sanye da sulke na kariya da hular kwano, ya shiga hannun hukuma bayan kisan da ya yi, kamar yadda kwamishinan ‘yan sandan Buffallo, Joseph Gramaglia ya bayyana a wani taron manema labarai a ranar Asabar.

Gramaglia ya ce mutane 10 ne suka mutu sannan mutum uku suka ji rauni sakamakon harin da matashin ya kai.

Kazalika, bayanai sun ce mutum 11 daga cikin wadanda lamarin ya rutsa da su bakar fata ne, lamarin da ya sa ake alakanta kisan da kiyayya ko wariyar launin fata.

Kwamishinan ya ce matashin ya harbe mutanen ne a wajen ajiyar motoci na katafaren shagon, kana ya kutsa ciki inda ya ci gaba da bude wuta kan mai uwa da wabi.

Daga cikin wadanda ya kashe har da wani tsohon jami’in dan sanda da ya ke aikin gadi a shagon sayar da kayayyakin.