Wani matashi mai suna Dauda ya rasa ransa sakamakon fadowa da ya yi daga bene mai hawa uku yayin da ya ke sharar bacci.
Lamarin ya faru da misalin karfe 12 na daren ranar Juma’a a yankin Oniyo, Ita Merin a Ilorin da ke Jihar Kwara.
- Rikicin Ukraine: Za a soma jigilar dawo da ’yan Najeriya gida a ranar Laraba
- Gwamnatin Abia ta yi wa al’ummar Gombe ta’aziya kan kisan Fataken Shanu
Binciken Aminiya ya gano cewa matashin wanda mai yankan kauna ta yi wa bazata, yana sana’ar sayar da kayayyakin motoci ne a kasuwar Jengbe da ke yankin Ita-Nma a Karamar Hukumar Ilorin ta Arewa.
Wani abokinsa mai suna Alfa Abdul, ya shaida wa Aminiya cewar, Dauda bai jima da samun ‘yancin cin gashin kansa daga wajen mai gidansa ba.
“Benen hawa uku gare shi, akwai inda suke yin bacci inda suna son hutawa. Bayan ya dawo daga gida saboda zafin da ake yi sai ya wuce can don ya huta ya samu bacci kamar yadda ya saba yi.
“Amma abun takaici magagin bacci ya debe shi ya fado.
“An yi kokarin kai shi asibiti amma tun kafin a karasa rai ya yi halinsa. Tuni aka birne shi kamar yadda addinin musulunci ya tanadar,” a cewarsa.
Baba Musa, shugaban kasuwar ya tabbatar da faruwar lamarin ga manema labarai a ranar Litinin.
“Tabbas lamarin ya faru, kuma mun shiga damuwa baki dayanmu,” in ji shi.