✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Wani makaho zai yi gudun kilomita 400 a kwanaki 9

Simon Wheatcroft wani makaho ne mazaunin Amurka da ke yunkurin yin gudun fanfaladi da tsawonsa ya kai mil 240 kwatankwacin kilomita 400 daga garin Boston…

Simon Wheatcroft wani makaho ne mazaunin Amurka da ke yunkurin yin gudun fanfaladi da tsawonsa ya kai mil 240 kwatankwacin kilomita 400 daga garin Boston na Amurka zuwa birnin New York. Idan aka kwatanta a Najeriya za kai nisan daga Abuja zuwa birnin Katsina. Sannan makahon ya yi niyyar da zarar ya isa birnin New York kuma zai fafata a gasar tseren gudun fanfalaki ta duniya.

Kafar watsa labaran wasanni ta BBCsports ta kalato cewa makahon dan kimanin shekara 26, ya samu makanta ne tun yana dan shekara 18. Sai dai ya fara ganin alamar makantar ce tun yana dan kimanin shekara 13 zuwa 14 amma bai daina gani ba sai da ya kai shekara 18 da haihuwa a lokacin da ciwon makantar ya ci karfinsa.
Makaho Simon ya ce bai taba tunanin yin tsrere a rayuwarsa ba, musamman a lokacin da yake gani, amma ganin yanzu ya zama makaho ta sanya shi yanke shawarar yin gudun fanfalaki, tunda shi a ganinsa, gudun ne ya fi masa sauki a kan dukkan wasannin da zai yi.
“Da farko na so na yi wasan hawa tsauni mai nisa ne (mountain) don abin da budurwata take so kenan, amma ganin na makance ta sa ba zan iya yin wasan ba don haka na yanke shawarar yin gasar tseren gudun fanfalaki”, inji Simon.
A yanzu dai Simon dalibi ne a Jami’ar Sheffield inda yake karatu a fannin tunanin dan adam (Psycology) kuma a Jami’ar ce ya fara koyon gudun fanlafaki da ta sa ya kware.
Sai dai kafar sadarwar ba ta ambaci takamaiman ranar da Simon zai fara yin gudun kilomita 400 ba, amma dai tabbataccen abu ne makahon zai gudanar da wannan tsere na kilomita 400 a cikin kwanaki 9.
Idan makahon ya yi wannan tsere, zai zama shi ne irinsa na farko da wani makaho ya taba yi a fadin duniya.