Wani abin tsautsayi ya samu shahararren mai wasan kwallon golf na duniya Tiger Wood a karshen makon jiya a Italiya bayan wani mai daukar hoto ya mangare shi da kyamar a baki ba tare da saninsa ba, al’amarin da ya sa ya rasa daya daga cikin hakoransa na gaba.
Rahoton da kafar sadarwar Naij.com ta kalato ya nuna, mai daukar hoton yana kokarin shiga harabar filin wasan tseren kankara ne don daukar hoton budurwar Tiger Wood mai suna Lindsey bonn bayan ta zama zakara a gasar tseren kankara na duniya da ya gudana a Italiya, kwatsam sai ya mangare Tiger Wood a baki wanda ya yi shigar burtu don kada ’yan jarida su dame shi, al’amarin da ya sa ya yi asarar hakorinsa na gaba.
Tiger Wood dai ya halarci gasar ce don taya budurwarsa mai suna Lindsey bonn murna saboda nasarar da ta samu na gasar tseren kankara na duniya a Italiya amma sai ya yi shigar burtu ta hanyar rufe fuskarsa al’amarin da ya sa da yawa daga cikin mutane musamman manema labarai da ke filin wasan ba su san yana wurin ba sai bayan da aka cire masa hakori.
Daga baya ne Tiger Wood ya yi wa budurwarsa bayanin abin da ya faru bayan ta tambaye shi yadda aka yi ya rasa hakorinsa na gaba.
Tuni mai daukar hoton da ya yi sanadiyyar rasa hakorin Tiger Wood ya aika masa sakon ban hakuri a kan abin tsautayin da ya faru kuma ya ce bai ji dadi ba yayin da Wood ya amince kuma ya ce kaddara ce ta kawo haka tun da ba da gangan ya aikata haka ba.