Hakika Allah Shi ne Gwani kuma Mai ba kowa arzikin da Ya so ta hanyoyin da dan Adam ya yanke kauna.
Gaskiya ne akwai mawaka da yawa cikin duniyar nan, kuma ana ganin arzikin da Allah Ta’ala Ya yi musu ta hanyar sana’ar waka, bari kawai mu dukufa kawai a Najeriya ta Arewa inda take da mawaka shahararru.
- Mahara sun sace matar ma’aikacin Poly da ’ya’yanta 3 a Kaduna
- Labaran Auratayya: Babana ne sanadin wahalar aurena!
A Arewa akwai mawaka wadanda suka yi fice sosai a duniyar wakokin Hausa, kususan na zube da masu sa hikimarsu kadai ta kotso, molo, garaya, kuntigi, goge da sauransu kamar kidan Danmaraya da mai irin muryarsa dan Zamfara Babangida Kakadawa.
To cikin mawakan nan akwai na zube, wato masu waka babu kida kuma a wancan zamani akwai na siyasa kususan jam’iyyar talakawa ta Malam Aminu Kano, wacce aka fi sani da NEPU.
Gaskiya NEPU tana da zakakuran mawaka wadanda suka yi suna kwarai da gaske har zuwan PRP wacce ta bullo lokacin Jamhuriya ta Biyu.
Ba sai an fada ba, domin a wancan zamani aka yi shahararren marubuci, kuma mawakin zube Dokta Sa’adu Zungur Allah Ya jikansa, amin.
Haka akwai zakakuran mawakan zube irin su marigayi Dokta Abubakar Ladan wanda mutumin birnin Zariya ne, kuma ya shahara wurin wake shugabannin Afirka na da, da kuma shiyyar da suka fito.
Alhaji Abubakar Ladan ya yi wa PRP waka cewa “Samarin kauye birni ku zabi Aminu dan talakawa”, wakar ta yi armashi sosai duk da Malam bai so wasu daga cikin baitukan wakar ba!
To komai ake ciki dai akwai mawaka wadanda Allah Ya ba su basira irin su Aminu Alan Waka wanda a yanzu tauraruwarsa take haske kamar gwanina wanda a dalilinsa na yi wannan rubutu wato Alhaji Dauda Kahutu Rarara Katsina.
Gaskiyar lamari Alhaji Dauda Rarara ya fara wakarsa ba ta siyasa ba ce, amma daga karshe ya zama zakakuri wurin wakokin siyasa wacce ta kai shi koli a yanzu.
Ba wai zuga wannan zakakurin mawaki nake ba, a’a gaskiya ce ta yi halinta inda wasu ba su san cewa Allah Ta’ala Shi ne Mai raya dan jariri sabon haihuwa a daji ya rayu ya zama sarki ba.
Subhanahu Wata’ala Yana yin ababe fiye da fahimtar dan Adam domin shi ma dan Adam yin sa ake yi ba tare da sanin shi wane ne ba.
Ka ga dai Mamman Shata, wanda shi ma mutumin Katsina ne kuma shahararren mawakin Hausa ga shi asalinsa Bafillace ne, a zamaninsa babu mawakin da ya shahara kamarsa cikin duniyar wake ta Hausa.
An ma ce duniyar kaf dinta mawaka uku su suka fi kowa a duniya – su ne Alhaji Mamman Shata da Alhaji Muhammad Rafi na kasar Indiya sai kuma Sheikh Muhammad Wardi na Sudan.
To ashe mu ma za mu samu wani mawakin shahararre mai suna Alhaji Dauda Kahuru Rarara a lokacin da su wadancan manyan mawaka suka koma ga Mahaliccinmu.
Allah Ta’ala Ya jikan wadancan Musulmin mawaka wadanda wakokinsu ba su kirguwa, domin yawansu.
Abin mamaki dukkansu Musulmi ne kuma daga sassan duniya daban-daban. To haka Allah Yake ikonSa, sai wasu mutane su shahara ta wurin da ba a zato.
Mu a nan Arewa ba kasafai muke daukar mawaka da daraja ba, domin kawai ana ganinsu maroka ne, masu kalangu da molo da sauransu, duk da cewa suna fadin abubuwa kamar zaurance, sai ka ga malamai a jami’o’i suna amfani da su a ilimance.
To shi wannan bawan Allah da na yi wannan makala dominsa, wato Dauda Kahutu Rarara mutum ne da ya jawo wasu kananan mawaka kusa da shi domin taimaka musu, su ma su yi irin tasu gwanintar a rayuwa.
Ganin haka ne ya sa su wadannan kananan mawaka suke girmama Alhaji Dauda Kahutu Rarara domin ba shi da mugunta kuma situdiyonsa kullum cike yake da mawaka gwanaye, don haka ne suke kiransa da Ciyaman wato shugaba; wannan kalmar saboda karamcinsa da taimakon jama’a ne.
Gaskiya Alhaji Dauda Kahutu Rarara mawaki ne na siyasa, kuma daukaka ta kai shi sama inda ta kai shi koli sosai kuma har yanzu zarensa kara kwari yake yi kuma Insha Allah babu lokacin tsinkewa.
Mutanen Kannywood, Ahuwonku! Alhaji Mamman Shata ya ce a cikin wakarsa ta Magaji Mai Ido Daya cewa: “Dila da kura da biri zaman dawa suka tara, amma halinsu ya bambanta.”
Kwamared Ibrahim Abdu Zango, shi ne Shugaban Kungiyar Kano Unity Forum, kuma za a iya samunsa ta: 08175472298.