✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Wani limami ya jagoranci mabiyansa Sallar Idi duk da rashin ganin wata a Nijeriya

Wannan ba shi ne karon farko da limamin yake bijire wa umarnin Majalisar Ƙoli ta Musulunci a Nijeriya ba.

Wani malamin Musulunci a Sakkwato, Sheikh Musa Ayuba Lukuwa ya jagoranci mabiyansa Sallar Idin karamar sallah a yau Talata.

Wannan dai na zuwa ne duk da mahukunta sun sanar da rashin ganin jinjirin watan Shawwal a jiya Litinin.

Bayanai sun ce wannan ba shi ne karon farko da limamin yake bijire wa umurnin Majalisar Ƙoli kan lamurran addinin Musulunci a Najeriya, musamman kan batun da ya shafi ganin watan Azumin Ramadan ko na Sallah.

A wannan shekara ma, Sheikh Lukuwa ya jagoranci magoya bayansa wajen gudanar da Sallar ta Idi a Masallacinsa da ke shiyar Mabera da sanyin safiyar yau Talata.

Limamin ya kafa hujjar yin sallah da kuma ajiye azumi bisa ga samun rahotannin ganin wata a wasu wurare da ya hakikance da su a Jamhuriyar Nijar, duk da yake ya ce a Najeriya ma an samu wasu rahotanni na ganin watan Shawwal sai dai ba a tantance su ba.

Wannan Sallar dai ta saba wa umurnin Sarkin Musulmi, Abubakar Sa’ad II wadda ya ayyana ranar Laraba 10 ga Afrilu a zaman ainihin ranar Sallar Idi, saboda ba a ga watan Shawwal ba ranar Litinin ta 29 ga Ramadan, saboda haka watan Ramadan zai cika kwana talatin ke nan.

Galibi dai kusan dukkan Musulmi a Najeriya sun cika azumi talatin kafin gobe Laraba su yi Sallar Idi.