✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Wani abun fashewa ya kashe mutum 4 a Sakkwato

Ana zargin wata tukunyar gas ce ta fashe a shagon wani mai walda.

Akalla mutum hudu ne aka tabbatar da mutuwarsu yayin da wasu uku suka samu munanan raunuka sakamakon fashewar wani abu a shagon walda a Karamar Hukumar Isa ta Jihar Sakkwato a yammacin ranar Lahadi.

Wani mazaunin yankin ya ce: “Lokacin da na ji karar fashewar wani abu mai karfi, abin da ya fado min a rai shi ne ’yan bindiga sun kai farmaki.

“Da na ga mutane suna gudu zuwa shagon walda inda abun ya fashe hankalina ya kwanta cewa ba ‘yan bindiga ne suka afka yankin ba.

“Da na yi bincike an sanar da ni cewa wani abu ne ya fashe a wani shagon walda kuma an samu asarar rayuka da jikkatar wasu da dama.”

Kakakin rundunar ’yan sandan jihar Sakkwato, DSP Sanusi Abubakar, ya tabbatar da cewa faruwar lamarin da kuma adadin wadanda abin ya ritsa da su a yammacin ranar Lahadi.

Abubakar ya ce, “fashewar ba ta da alaka da kalubalen tsaro da ke addabar yankin; fashewar wata tukunyar gas a shagon wani mai walda a yankin ya yi sanadin mutuwar mutum hudu.

“Wasu uku da suka samu raunuka kuma suna cikin mawuyacin hali, amma suna samun kulawa a wani asibiti da ba a bayyana sunansa ba a jihar.”