✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Mabiya Abduljabbar sun yi tir da masu katsalandan ga karar da ya daukaka

Mabiyansa sun zargi wasu Malaman Kano da yi wa shari'arsa katsa-landan.

Mabiyan Sheikh Abduljabbar Nasiru Kabara sun yi tir da wani yunkuri suke zargin ana yi na kawo cikas ga karan  da ya daukaka kan hukuncin kisa da kotun yanke masa.

Ibrahim Abdullahi Warure, wanda ya yi magana a madadin mabiyan a wani taron manema labarai a ranar Lahadi a Kano, ya zargi wasu malamai da kara matsin lamba na yin watsi da karar.

A cewar Warure, Malaman suna kara matsa lamba ga gwamnati mai jiran gado da kuma kotu da su goyi bayan hukuncin kisan da aka yanke masa.

Ya ce mabiyan za su ci gaba da daukaka karar a gaban babbar kotun Jihar Kano har sai an yi wa malamin nasu adalci.

A cewarsa, wannan hakki ne da ba za a tauye wa malamin ba kamar yadda kundin tsarin mulkin Najeriya ya tanada.

Ya shawarci malaman da yake zargi da su bar kotu ta yi aikinta ba tare da tsangwama ba.

Warure ya ce “Muna yin Allah wadai da katsalandan da suke yi  kan malaminmu da kuma barazanar da suke yi wa kotu wanda muke ganin tamkar cin fuska ne ga kotu da gwamnati,” in ji Warure.

An daure malamin ne a ranar 17 ga watan Yuli, 2021 a gidan yari bisa samun sa da laifin yin kalaman batanci ga Manzon Allah (SAW).

Daga bisani kuma wata kotun shari’ar Musulunci da ke Kano ta yanke masa hukuncin kisa ta hanyar rataya a ranar 15 ga watan Disamba, 2022.

Ya daukaka kara kan hukuncin kisa da aka yanke masa a gaban wata babbar kotu a jihar.