Wadannan sharudda hudu wajibi ne a kiyaye su a lokacin tuba, ba wai kawai furuci ne da baki ba, a’a da kulla niyya a zuciya lokacin da za a yi tubar cewa mutum ba zai koma ga aikata wannan zunubi ba, tare da yin nadama kan abin da ya gabata na sabo ko barna ko zunubin da yake yi. Idan kuma akwai hakkin wani da ya tauye kamar dukiya ko mutunci to ya mayar wa mai ita ko ya nemi afuwansa. Idan kuma ba zai iya kaiwa ga mai dukiyar ko wanda ya ci mutuncinsa ba, to sai ya ware kwatankwacin dukiyar ya sadakar a madadinsa kuma ya yi ta istigfari kan haka da kuma neman gafarar Allah kan mutuncin wanda ya ci.
A nan ga wata kissa game da yadda zunubi ke kai ma’abucinsa ga hallaka domin mu yi nazari a kai:
“Wata rana bayan an tafka ruwan sama sai wani daga cikin magabatana kwarai mai suna Hisham bin Hasan yana tafiya a bayan Al’ala bin Ziyad a wata hanya mai tabo a kauyensu. Sai ya lura Ziyad yana kauce wa ruwan da yake gudu a gefen hanya tare da tabon, yana cikin wannan tsantseni sai wani mutum ya tunkude shi har takalminsa ya zame ya ja shi cikin wannan ruwan. Kuma igiyar ruwan ta ja Ibn Ziyad zuwa daya gefen hanyar.
Bayan sun isa gida sai Ibn Ziyad ya juyo zuwa ga Hisham ya ce: “Yadda muke kauce wa tabo da igiyar ruwan nan a kan hanyarmu ta zuwa gida, haka ya kamata Musulmi ya kauce wa saba wa Allah a daukacin tafiyar da yake yi zuwa Lahira. Kuma kamar yadda ka ga igiyar ruwan nan ta ja ni, haka igiyar zunubi take jan mutum lokacin da ya fada cikinta, za ta yi ta jan sa tana dulmiyar da shi yana dada nutsewa.” Inna lillahi wa inna ilaihi raji’un! Mu lura idan igiyar ruwa ta rinjayi mutum ba ya iya yin komai, haka in zunubi ya rinjayi mutum babu abin da zai iya, don haka ake son a kullum ya rika taka-tsantsan kada ya yarda zunubin nan ya rinajye shi ya kai shi ga hallaka. Ke nan a daukacin rayuwar dan Adam ya wajaba ya rika taka-tsantsan ne yana kauce wa duk abin da ya san Allah Ya haramta masa wanda shi ne misalin tabo da kazanta da ba mu so mu fada a ciki, yayin da rayuwa kuma kamar ruwan da ke koro tabo da kazanta ne, sannan son zuciya kuma tamkar shi ne igiyar ruwan ne da ke jan mutum, shi kuma mutum yana kokarin kwacewa har ya tsira ko ya hallaka.
Har wa yau game da tuba da komawa zuwa ga Allah akwai wani abin misali da wani abu da ya faru da Bani Isra’ila a karkashin jagorancin Annabi Musa (Alaihis Salam), lokacin da Fir’auna ya dauki matakin karshe na gamawa da su.
Mu rika kallon ga Annabi Musa (Alaihi Salam) nan yana jagorantar tsofaffi maza da mata da kananan yara na al’ummar Bani Isra’ila da suke gudun darkakewar Fir’auna, mu kalle su ga su nan sun nufo bakin teku, ba su da jirgin ruwa, ba su da ko da kwale-kwalen da za su hau domin su tsira, kuma ba su da makamin da za su iya juyawa su fuskanci Fir’auna da rundunarsa wadanda suka taso su a gaba da nufin darkake su. Ga nan Fir’auna da wannan runduna cikin fushi. Ga Bani Isra’ila a karkashin Annabi Musa (Alaihin Salam) sun iso bakin teku ruwa iya kallonsu, ga su nan sun waiwayawa baya, sun hango Fir’auna cike da fushi, mayakansa rike da miyagun makamai, sukwane a kan dawaki sun nufo su. Ganin wannan hali na tsaka-mai-wuya da suke fuskanta sai suka koka ga Annabi Musa (Alaihis Salam) kamar yadda Alkur’ani Mai girma ya ba mu labari: “Sa’an nan a lokacin da jama’a biyu suka ga juna, sai sahabban Musa suka ce: “Lallai ne mu, hakika, wadanda ake riska ne.” (K:26:61).
To amma Annabi Musa (Alahis Salam) ya san Allah ba zai bari a shafe da’awar Musulunci a bayan kasa ba. Sai Allah Ya ba mu labarin amsar da Annabi Musa (Alaihis Salam) ya ba su, amsar da take nuna karfin imani irin na Annabawa da Manzanni (Alaihimus Salam) Allah Ya ce a harcen Annabi Musa (Alaihis Salam): “Ya ce “Kayya! Lallai ne Ubangijina Yana tare da ni, zai shiryar da ni (hanyar tsira).” (K:26:62).
Nan take sai Allah Ya umarci Annabi Musa (Alaihis Salam) cewa: “Sai Muka yi wahayi zuwa ga Musa cewa: “Ka doki teku da sandarka.” Sai teku ya tsage, kowane tsagi ya kasance kamar falalen dutse mai girma. Kuma Muka kusantar da wadansu mutane (su Fir’auna) a can. Kuma Muka tserar da Musa da wadanda suke tare da shi gaba daya. Sannan Muka nutsar da wadancan (su Fir’auna).” (K:26: 63-66).
A daidai wannan lokaci da Fir’auna ya ga kansa a tsakiyar teku ya tabbata mutuwa ta zo masa, sai ya ce: “Na yi imani cewa, hakika, babu abin bautawa face wannan da Banu Isra’ila suka yi imani da Shi. Kuma ni ina daga Musulmi (masu mika wuya ga Allah).” (K:10:90).
Ibnu Abbas ya yi ce a ranar da Fir’auna ya fada cikin teku kuma ya fahimci cewa zai mutu, sai ya yi kokarin tuba, amma sai Mala’ika Jibril ya zo masa ya rika rika watsa wa fuskarsa tabo yana cika masa baki da shi, don kada ya samu damar rokon rahamar Allah, wanda da ya roka da an ba shi.
Allah Ya fada wa Fir’auna da sauran mutanen da ba su tuba sun koma ga Allah ba, sai lokacin da mutuwa ta zo cewa: “Ashe a yanzu (ne za ka tuba ka yi imani)! Alhali kuwa hakika ka saba a gabani, kuma ka kasance daga masu barna?” (K:10:91).
Abin da muke so mu ciro daga wannan kissa ta mutanen Annabi Musa (Alaihis Salam) shi ne cewa kada wani bawa ya jinkirta tuba zuwa wani lokaci da yake ganin shi ya fi dacewa ya tuba. A’a ya tuba nan take, ya tuba a kowane lokaci da niyyar ba zai koma ga aikata laifin da ya san yana aikatawa ba. Kada ya ce, sai gobe ko sai jibi ko sai bayan wata ko sai badi. Kada ya ce sai ya tara kudi kaza ko ya mallaki kadarori kaza sannan zai tuba daga wata barna ko sabo da yake samu daga gare shi.
Dan Adam ya fahimci cewa rayuwa da mutuwa suna hannun Allah ne, bai san yaushe mala’ikan mutuwa zai ziyarce shi ya amshe ransa ba. Kada mutum ya ce ba zai tuba ba sai ya ga kansa a wani matsayi na rashin jin dadi ko na rashin lafiya ko na hadari. Gaggauta tuba abu ne da yake wajibi, jinkirta tuba laifi ne mai zaman kansa, wato ya zama laifi biyu na zunubin da ya aikata da na rashin tuba.
Shaidan zai rika fisgar bawan da ya tuba ya sake komawa ga zunubi ko barna, duk da haka kada bawa ya ce ba zai tuba ba, ci gaba da tuba ku yi ta kokuwa da Shaidan, shi ne misalin igiyar ruwan nan da muka ambata. Idan ka samu a karshe ka mutu a kan tuba ka samu nasara a kan Shaidan ke nan, idan kuma ka bari ya rinjaye ka, shi ke nan ya samu nasara a kanka.
Allah Ya sa mu dace