A cikin shekara 15 daga shekarar 2009 zuwa 2024 Arewacin Nijeriya ya samu kansa a wani yanayi na ni-’ya-su, inda ya canza daga yanki mai inganci zuwa yankin da ke fama da matsin tattalin arziki yayin da kuma aka bar yankin a baya ta kowace fuska.
Duk da cewa yankin ya yi fama da matsaloli masu yawa, amma abin da ya faro daga shekarar 2009 inda aka fara fuskantar matsalar tsaro a yankin Arewa maso Gabas, lamarin da ya watsu a sauran sassan kasar nan da kuma matsalar ’yan bindiga da na tattalin arziki sai lamarin ya zama tarnaki ga duk bangarorin rayuwa.
- Mawaƙin siyasa Garba Gashuwa ya rasu
- Muna zargin ’yan gwangwan da satar wayoyin lantarki da janaretoci a Osun – ’Yan sanda
Wadannan abubuwan sun gurgunta harkar noma, sun kuma lalata harkar kasuwanci sannan sun sa an rufe makarantu da dama wanda hakan ya sa adadin yaran da ake sanyawa a makarantu ya ragu.
Wannan koma-baya ya shafi walwala da jin dadin rayuwa, ya kuma dakile ci gaban kasa sannan ya sauya rayuwa gaba daya.
Za a iya cewa ko zanga-zangar da ta gudana a fadin kasar nan mai taken kawo karshen mummunan shugabanci, yankin Arewa ya ga zurfin tabarbarewar al’amura da yadda ta shafi akasarin kowane dan Arewa.
Yayin da sauran bangarorin kasar nan suka yi zanga-zangar a kan tituna ba tare da cutarwar kirki ga daidaikun mutane ko lalata kayan jama’a ko na gwamnati ba, a Arewa lamarin ya sha bamban inda aka samu adadi mai yawa na kai hare-hare a kan mutane da sace kayayyakin gwamnati da daidaikun mutane tare da lalata wasu kayayyakin
Wannan ya sa da yawa daga cikin manyan Arewa suka bukaci a sake wayar wa ’yan Arewa kai.
Jim kadan da zanga-zangar, Mataimakin Shugaban Kasa Kashim Shattima ya bukaci a yi zama na musamman da masu ruwa-da-tsaki na yankin don samo hanyoyin da za su bunkasa ci gaban Arewa.
“Za mu bukaci goyon baya daga dukkan yankuna da shugabannin siyasa wadanda suka damu da ci gaban Arewa,” in ji shi.
A makon jiya kuma, wata kungiya da aka fi sani da Kungiyar ’Yan Dimokuradiyyar Arewa (League of the Northern Democrats), da Dokta Umar Ardo ya shirya taronta wadda ake gani a matsayin wata kungiya ta ’yan bokon Arewa sun gana don tattauna matsalolin da ake fama da su a Arewa.
Shugaban Kungiyar kuma tsohon Gwamnan Jihar Kano, Malam Ibrahim Shekarau, ya ce Arewa ta gano tana da tarin matsaloli a tare da ita wadanda wajibi ne a hada kai a tunkare baki daya.
Ya ce ya kamata mutane su ajiye son rai da bambanci a gefe, su zo su hada hannu don amfanin yankin.
Wadannan yunkuri suna faruwa ne sakamakon gano nakasun da yankin ya samu bayan zanga-zangar da ta gudana, wanda in ba a yi wa tufkar hanci ba zai iya lalata yankin da yake da a baya yake da tsari da hadin kai wajen fuskantar abubuwan da suke shafar mutanensa.
A zanga-zangar da ta gudana daga ranar 1 zuwa 10 ga watan Agusta, matasa sun yi kunnen uwar shegu da shawarwarin malamai da ’yan siyasa da sarakuna da kuma manyan jagororin kasa da masu ruwa-da-tsaki, suka bi abin da ransu ke so, wanda kuma bai amfanar da Arewa da komai ba sai shafa mata kashin kaji a idon duniya.
Wasu daga ciki sun nuna yanayin da Arewa ta samu kanta a ciki na da alaka da koma-bayan shugabanci da kama-karya a tsakanin ’yan siyasa da dogaro a kan kudin shiga na man fetur da wulakantar da harkar noma da rashin ilimi da kuma yawaitar cin hanci da rashawa.
Daya daga cikin shugabannin Arewa, Sanata Ibrahim Ida, Wazirin Katsina, ya ce matsalar Arewa tana da alaka da rashin kyakkyawar alaka a tsakanin manyan da matasan Arewa.
“Mafiya yawan wadanda suke kusa da madafun iko ko wa’azantarwa sa’o’in wadanda suke wayar wa kai ne,” kamar yadda ya fada a hira da jaridar Aminiya.
Ya kara da cewa, wannan ba haka yake a baya ba, domin akwai banbanci a tsakanin wadanda ake mulka da masu rike da madafun iko.
Babban Limamin Masallacin Juma’a na Alfurkan da ke a Titin Alu Avenue a birnin Kano, Dokta Bashir Aliyu Umar, ya goyi bayan ra’ayin Wazirin Katsina, inda ya ce ’yan siyasa suna wasa da hakkokin jama’a.
Shugaban Kungiyar Middle Belt Forum (MBF), Dokta Pogu Bitrus, a bangarensa ya ce Arewa ta kasa tsayawa da kanta saboda rashin adalci wanda ya mayar da wasu daga cikin yankunanta baya.
“Wasu daga cikin matsalolin an gaje su ne daga Turawan mulkin mallaka, wadanda suka tabbatar wasu mutane sun mamaye wasu ta hanyar mulki ta bayan fage; wannan ne ya kawo mu yanayin da muke ciki a yau,” in ji shi.
Amma ga Farfesa Munzali Jibrin fitaccen malamin jami’a da ya yi ritaya, tashe-tashen hankali da sauran abubuwan assha da suka faru a lokacin zanga-zangar sun faru ne saboda watsi da aka yi da matasa, wadanda ke zaman kashe wando.
“Wadannan mutane ne fa da ba su da wata makoma, ba ilimi, ba wata sana’a da za su iya dogaro da ita,” in ji shi.
Abin da ya biyo baya shi ne maimakon a ce yankin Arewa ya rike matsayinsa na kyakkyawan ci gaba sai ya zama mai bayar da tsoro ga al’umma.
Misali yankin ya yi shahara wajen yawaitar wadanda ba su zuwa makaranta da yawan matan da ke mutuwa a wajen haihuwa da rashin gine-ginen makarantu da asibitoci da rashin aikin yi ga kuma uwa-uba rashin tsaro.
Kwararru sun ce hakan bai kamata ba, lura da dimbin albarkatun kasa da sauran abubuwan da za su hanzarta ci gaban yankin da suke jibge a cikinsa.
Tsohon Ministan Noma Alhaji Sani Zangon Daura ya taba tabbatar da haka a wata hira da gidan talabijin na Trust TV, ya ce Arewa tana da dalilan da za ta tsaya da kafarta, lura da abubuwan da Allah Ya albarkaci yankin da su.
“Duk wasu abubuwa na bunkasa tattalin arziki suna Arewa. Muna da kusan kashi 80 na fadin kasa, wanda kowa ya san fadin kasa babbar albarka ce.
“Na biyu kuma mafi muhimmanci shi ne, idan za a gudanr da kidayar da ba ta siyasa ba a cikin gaskiya, ko mutanen Kudu sun san fiye da kashi biyu bisa uku na mutanen Nijeriya suna Arewa ce.
“To idan ka samu wadannan abubuwa biyu, fadin kasa da yawan jama’a kai ne a sama. Kusan ko’ina a Arewa Allah Ya ba mu albarkatun ma’adinai,” in ji shi.
Kari a kan haka daga cikin jihohi 36 na kasar nan, 19 duka suna Arewa ce, wanda kai-tsaye na nufin yankin na da abubuwan ci gaba wajen gudanar da mulki kamar yawan kananan hukumomi da mazabu daban-daban.
Game da abubuwan da suke ci wa yankin Arewa tuwo a kwarya wanda ya sa yankin ya zama cikin annoba ne ya sa wasu kungiyoyi da daidaiku suka yi kokarin ganin sun taimaka ta hanyar hada kai domin neman hanyar warware matsalolin sai dai har yanzu wannan buri bai tabbata ba.
Kungiyar Kare Muradun Arewa (ACF) wadda aka kafa don hada kan shugabannin Arewa don magance matsalolin da suke tasowa a yankin ta yi kokarinta a baya.
Gwamnonin yankin sun kafa Kungiyar Gwamnonin Arewa don hada kai su gano matsalolin yankin nasu da kuma lalubo hanyoyin magance su.
Haka an kafa Kungiyar Dattawan Arewa (NEF) da irin waccan manufa wadda ita ma ta yi kokari kan haka.
Sai da matsalolin da ake fuskanta sun gagari Kundila, ta yadda maimakon magance su, sai ma karuwa suke dada yi.
Mutane da yawa suna tuno yadda yankin Arewa yake a lokacin mulkin Sardaunan Sakkwato Sa Ahmadu Bello.
A wancan lokaci aka gina cibiyoyi kamar Jami’ar Ahamdu Bello da ke Zariya, Rediyon Nijeriya na Kaduna, Kamfanin Buga Jaridun New Nigerian da Gaskiya Ta Fi Kwabo (NNN) da Hukumar Bunkasa Arewa, yanzu Kamfanin Bunkasa Zuba Jari na Arewa (NNDC); wanda ya samar da sakandarori a sassan yankin da bayar da gurabun karatu a ciki da wajen kasar nan ga ’yan Arewa.
Kuma bayan Sardauna, shugabannin Arewa sun yi kokarin ganin wannan lamari ya ci gaba inda suka janyo hankalin masana’antu da suka hada da Matatar Mai ta Kaduna (KRPC) da Kamfanin Mulmula Karafa na Ajaokuta da Kamfanin Buga Takardu na Jebba da Kamfanin Karafa na Jos da Kamfanin Harhada Motocin Fijo a Kaduna da masaku a Kaduna da Kano da Kamfanin Harhada Motoci na Styer a Bauchi da kuna kamfanonin siminti ne Binuwai da Ashaka a Gombe.
Mutane da yawa za su iya tunawa a lokacin da abubuwa suke tafiya daidai yanayin na da kyau yadda masu zuba jari suka rika darawa kamar ’yan kasuwar da suka hada da Alhaji Mai Daribe da Alhaji Alin Kotoko da Alhaji Bello Mohamed Bagudu, Wazirin Nupe da iyalan Dantata da Alhaji Isyaku Rabi’u da Jerome Tilley Gyado da DB Zang da Yarima Samuel Adedoyin da sauran ’yan kasuwa ’yan kasa da dama.
Sai dai abi da ke faruwa a yanzu a bayyane yake cewa ribar da aka samu ta salance bayan da alamu suka nuna Arewa tana makyarkyatar mutuwa.
Yadda Arewa za ta dawo da matsayinta
Wasu suna ganin cewa idan har Arewa za ta dawo cikin hayyacinta sai yankin ya magance tsarin samar da shugabanci.
Sanata Ida yana daga cikin mutanen da ke dora alhakin tabarbarewar Arewa a kan tsarin jagoranci inda ya ce “Yayin da muke bukatar shugbanci mai karfi, lamarin zabar shugabanni ya zama wani abu daban.
“Mun kasa gane bambanci a tsakanin cancanta da dacewa. Dacewa shi ne duba yadda mutum ya taso da kuma irin abin da zai iya yi.”
Ra’ayinsa ya yi daidai da na Farfesa Munzali Jibrin wanda ya ce Arewa ba ta da mutanen da za a kira shugabanni, wadanda za su kawo wa yankin agaji a kan al’amuran da suka shafe ta.
“Mutane da yawa suna tsoron shiga cikin wasu lamura tsoron za su bata mutuncinsu da kimarsu, haka kuma akwai mutanen da suka sayar da mutuncinsu.
“Saboda dattijan da muke da su yanzu ba za su iya tsayawa da kafarsu ba.
“Lokaci-lokaci za ka samu suna zuwa wurin shugabannin da ke kan mulki don neman taimako a kan wasu abubuwa don haka sun sayar da mutuncinsu,” in ji shi.
Wasu kuma suna ganin akwai bukatar a kara ba fannin ilimi muhimmanci da samar da ayyukan yi ta hanyar farfado da masana’antu da bunkasa su tare da samar da yanayi mai kyau ga masu zuba jari don ci gaban yankin.
Babban Limamin Masallachin Alfurkan ya ce a yi gaggawar magance matsalar rashin aikin yi.
“Ya kamata a sanya koyon sana’o’i a tsarin koyarwa a makarantu don matasa su samu madogara,” in ji shi.
Game da batun tsaro Janar Martin Luther Agwai ya yi amanna cewa gano dalilan da suka janyo bacin rai ne zai taimaka wajen yin maganin lamarin.
“Kafin ka fara yarjejeniya ka fara samo dalilan da suka janyo wannan bacin rai sannan a magance su, idan ka san wadannan dalilai zai zama da sauki idan aka tashi magance matsalolin,” in ji shi.
Sauran mutane kamar su Dokta Bitrus sun bayar da shawarwari cewa idan har ana so Arewa ta koma yadda take a baya, dole sai dukkan masu ruwa-da-tsaki sun hadu sun ajiye dukkan wasu bambance-bambancen da suke tsakaninsu su dunkule su zama tsintsinya madaurinki daya.
A yanzu Arewa tana bukatar a yi mata wankan tsarki sannan ƙoƙarin da zai zo daga dukkan ɓangarori zai taimaka wajen dawo da yankin cikin hayyacinsa.