Ficewar da wadansu ‘ya’yan jam’iyyar PDP suka yi daga wurin babban taron jam’iyyar na musamman da aka gudanar ranar Asabar da ta gabata a Abuja abin kunya ne, musamman da yake shugaban jam’iyyar Alhaji Bamanga Tukur kafin wannan al’amarin ya faru ya yi hasashen cewa za a dinke barakar da ta kunno kai a cikin jam’iyyar tasu.
Tun lokacin da Bamanga ya zama shugaban jam’iyyar PDP yake cewa za a sasanta tsakanin ’ya’yan jam’iyyar, amma maimakon sasantawar barakar sai kara fadada take yi. Yanzu dai an rasa wannan damar saboda yadda gwamnoni bakwai da tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar suka bi wata tsararriyar hanya suka fice daga wurin wannan taron ba karamin abun mamaki ba ne.
Shi ma shugaba Jonathan wannan ficewar da masu korafin suka yi har ma suka fito da wata sabuwar jam’iyyar PDP da za ta yi hamayya da ta Bamanga ta kunyata shi, domin hakan ya faru ne kasa da sa’a guda da ya yi bayanin da ke nuna cewa babu jam’iyyar da kai PDP zaman lumana da kwanciyar hankali a wannan janhoriyar. A wannan ranar ta Asabar Jonathan ya samu gangara inda ya yi wadansu bayanai masu jawo hankali game da wanzuwar PDP. Inda ya yi wadansu tambayoyi da dama ga mahalarta taron, yana cewa, jam’iyyar PDP ta canja sunanta? Ta canja tambarinta? Ta canja manufarta? Ta canja burinta? Su kuma mahalarta taron suka rika amsawa da karfi suna cewa a’a. A nan shugaban kasa ya yi magana abin dubawa, domin idan aka lura za a ga cewa jam’iyyu biyu da suka fito tun farko tare da PDP, watau APP da AD tuni sun yi ta canja sunayensu da tambarorinsu ta yadda har ba a iya gane su yanzu. Sai dai kuma cikin sa’a guda da yin wannan jawabi na shugaban kasa da aka yi ta yi masa tafi, sai maganganun nasa suka koma holoko hadarin kaka.
Da yake jawabi a Cibiyar ‘Yar’aduwa da ke Abuja, watau wurin da masu korafi suka koma suka yi nasu taron, shugaban sabuwar jam’iyyar PDP Alhaji Abubakar Kawu Baraje ya ce sun kafa sabuwar PDP ce domin kubutar da jam’iyyar PDP daga mulkin kama-karya da rashin bin doka da kuma mayar da wadansu saniyar-ware da Bamanga Tukur yake yi tare da goyon bayan shugaban kasa domin cim ma burinsa a shekarar 2015. Ana iya kallon sabuwar jam’iyyar PDP a matsayin wata ‘yar karama idan aka kwatantata da tsohuwar jam’iyyar PDP, amma shugabanninta idan suka ce sune suke da rijaye sun yi aron wani salo ne da PDP da fadan shugaban kasa suke amfani da shi, inda suka ce kuri’un gwamnoni 16 a zaben majalisar gwamnonin kasar nan da aka yi kwanakin baya sun fi na gwamnoni 19, domin haka ba za a yi mamaki ba idan gwamnoni bakwai da suka bijire suka ce su ne suka rijayi gwamnoni 16 da suka rage a cikin tsohuwar jam’iyyar PDP.
Shugabannin tsohuwar jam’iyyar PDP za su iya nuna kamar ba su damu da wannan matsalar ba, sai dai kuma rashin gwamnoni guda bakwai tare da Atiku Abubakar da Bukola Saraki da kuma dimbin ‘yan majalisun tarayya a lokaci guda tamkar naushe ne da aka yi wa dan dambe a haba a yayin da ake dambe. A lokacin yakin cacar baki akwai lokacin da a siyasar Amurka aka rika tambaya shin wane shugaban kasa ne ya rasa wata kasa ga masu juyin-juya-hali? Ana cewa, ‘’wane ne ya rasa kasar china? ‘’ Truman ne! ‘’wane ne ya rasa kasar Cuba?’’ Eisenhower ne! ‘’wane ne ya rasa kasar Iran?’’ Carter ne! ‘’wane ne ya rasa kasar Grenada?’’Reagan ne! Yanzu idan wadanda suka shugabanci jam’iyyar PDP guda tara suka zauna domin su dora laifi a tsakaninsu dangane da wanda ya jawo wa jam’iyya asara a tarihin kafuwarta, tambayar ‘’wane ne ya jawo wa jam’iyyar PDP asarar gwamnoni bakwai?’’ me yiwuwa za ta taso, kuma amsar da za a bayar nan da nan ita ce: Bamanga ne! Ba gwamnoni bakwai kawai ya rasa ba, ya kuma rasa Obasanjo da Atiku da kuma ‘ya’yan jam’iyyar PDP da ke yankin kudu maso yamma.
Idan ‘ya’yan sabuwar PDP suka koma jam’iyar APC za a samu matsala saboda za su yi wa jam’iyyar nauyi domin za su shiga jam’iyyar ce tare da dimbin magoya bayansu ga kuma kudi. A halin yanzu ana ganin magoya bayan Buhari da Tinubu ne suka mamaye jam’iyyar, kuma kodayake jam’iyyar APC tana da gwamnoni goma sha daya duk da haka ba su fi karfin Buhari da Tinubu ba,domin kuwa mafi yawan gwamnonin ACN suna ganin Tinubu a matsayin ubangidansu ne a siyasance. Sai dai kuma wannan al’amarin zai canja idan yawan gwamnonin ya karu zuwa goma sha takwas.
Kodayake shugabannin sabuwar jam’iyyar PDP suna nuna cewa mulkin kama-karya da shugaban PDP Bamanga Tukur yake yi ne ya tilasta su ballewa daga jam’iyyar,amma babban dalilin rikicin jam’iyyar PDP shi ne gwagwamayar zaben 2015. Idan wadannan gwakmnonin suka koma jam’iyyar APC za su shigar da tsarin nan nasu da suka yi amfani da shi a jam’iyyar PDP wanda ke nuna cewagwanoni ne suke da ikon tabbatar da wanda zai tsaya takarar shugabancin kasar nan. Shi kuwa shugaba Jonathan wanda ya nace sai Bamanga ya cigaba da shugabancin jam’iyyar PDP duk da cewa ya kama hanyar ruguza ta, yana yin haka ne domin ya samu cikakken iko da jam’iyyar domin a sake zabensa ya tsaya takara a zaben fidda gwani. A sakamakon ballewar dimbin ‘ya’yan jam’iyyar PDP, wanda ba a taba samun irinsa ba tun daga janhoriya ta daya, al’amari ya sukurkuce wa Jonathan ke nan, wanda ya sanya a lokacin da ya koma gida ya kwanta bayan an daga taron a ranar Asabar ga alama ya rika tambayar kansa wannan tambayar, shin Bamanga ne zai fi amfani a gare ni a lokacin zabe ko kuwa gwamnono bakwai din nan?
Wane ne ya rasa gwamnoni bakwai?
Ficewar da wadansu ‘ya’yan jam’iyyar PDP suka yi daga wurin babban taron jam’iyyar na musamman da aka gudanar ranar Asabar da ta gabata a Abuja…