A ’yan kwanakinnan labarai sun bayyana daga wata kafar yada labarai mai zaman kanta a Kano, da ta yi shaguben ana binciken wani babban jami`in `yan sanda da ya zauna Kano, ya kuma yaki barayin shanu, a kan badakalar sace shanun da ya jagoranci rundunarsa ta kwato daga barayin shanu a jihar, musamman daga dajin Falgore. A ci gaba da labarin kashegari, kafar labaran ta dan buda wa masu saurare da har suka fara zargin tsohon Kwamishinan `yan sandan jihar, yanzu kuma Mataimakin Sufeto Janar mai kula da tashoshin jiragen ruwa da ke Legas, AIG Muhammad Musa Katsina take nufi. A nan ta tsaya ba tare da ta iya tantance wa masu saurare ba yawan shanun da ake zargin babban jami’in ’yan sandan ya yi awon gaba da su ba, balle kuma abin da binciken ya gano na gaskiya ko rashin gaskiyar zargin da ake yi masa, sai dai ta ce a bi ta bashi.
Kamar yadda na fadi a sama waccan kafar yada labarai ba ta fayyace kowane babban jami`in dan sanda ba ne ake zargi da har ta kai ta ce yanzu ana bincikar rawar da ya taka, amma yanzu alamu sun fara nuni da cewa tsohon Kwamishinan ’yan sandar jihar kuma AIG Muhammad Musa Katsina ake zargi da kore wasu daga cikin dubban shanun da ya jagoranci kwatowa a jihar.
Shi dai AIG Musa Katsina, Jihar Kano ita ce jiha ta hudu kuma ta karshe inda ya zauna a zamansa na Kwamishinan ’yan sanda, bayan jihohin Kogi da Imo da Oyo. A jihar Kano inda nan ya samu karin girma na mukamin AIG, wato Mataimakin Sufeto Janar. Jihar Kano da nan nike da zama sama da shekaru 30, don haka ita na fi sanin irin aikace-aikacen da ya yi na tsaron doka da oda, tun zuwansa a farkon watan Satumbar bara da kuma tashin a cikin watan Maris din da ya gabata watanni shidda ke nan. Ya tarar da jihar a matsayin kusan dukkan matakan tsaro a tabarbare, tana fama da annobar cin zarafin mata, musamman fyade a kan kananan yara da sace ko yin garkuwa da mutane, don neman kudin fansa ga sace-sacen shanu da ya yawaita, ga matsalolin fatauci da shan miyagun kwayoyi, musamman ga matan aure, baya ga sauran ayyukan ta`addanci.
Alal misali, a kan batun sace-sacen shanu da yin garkuwa da mutane da zakke wa matan aure ta karfin tsiya daga irin wadancan miyagun mutane, sai da ta kai fagen da mutanen kauyuka irin su Murmushi da Karasa da Zinabi da Gazobi da Gidan Kare da `Yantagwaye da Sabon-garin Makwasa da Makwasa da Burum-Burum da Sitti da Masu da wasu kauyuka da ke makwabtaka da su, da suke cikin hurumin kananan Hukumomin Sumaila da Doguwa, sun zama a tarwatse, mutane ba sa iya kwana a gidajensu, inda kuma suke kwanan, to, kwana ne na cikin zullumi da fargabar za a kawo musu hari ko a sace musu dabbobinsu da dukiyoyinsu ko su ma kansu, harkokin kasuwanci sun tabarbare haka ma na zamantakewa irin su yin suna ko daurin aure.
A irin wannan yana yi, bayan tattaunawa da Gwamnan Jihar Kano, Dokta Abdullahi Umar Ganduje da Mai martaba Sarkin Kano, Alhaji Muhammadu Sanusi II, da sauran masu ruwa da tsaki na cikin al’umma da jami`an tsaro da ke jihar da AIG Musa Katsina ya yi, sai ya daura damara ya fara kafa Kwamitoci daban-daban don tunkarar yadda za a shawo kan wannan mummunar annoba ta tabarbarewar tsaro a jihar, ta yadda kusan dukkan Kwamitocin da ya kafa su ne na farko a jihar da rundunar ’yan sanda a jihar ta taba kafawa. Kwamitocin da akasari shi da kansa ya rinka jagorantarsu.
Alal misali AIG Musa Katsina shi ne Kwamishinan farko da ya a taba kafa Kwamitin yaki da barayin shanu ya kuma shugabanci Kwamitin wajen shiga lungu da sako na inda duk aka san maboyar barayin ce da shanun da suka sace, musamman dajin Falgore ana kama su daya bayan daya da shanun da suka sace. Jagorancinsa ne ya jaza aka kama barayi 253, da kwato shanu da sauran dabbobi har dubu bakwai da 897, da muggan makamai da suka hada da bindigogi iri-iri. Daga cikin wancan adadi na barayi ne aka samu 46, da suka amsa shirin tayin afuwa na gwamnatin jihar, bayan sun mika makamansu da sunan sun tuba.
AIG Musa Katsina a zamansa na Kwamishin ’yan sanda a cikin tsawon watanni shidda a Kano shi ya fara kafa bangaren binciken cin zarafin mata, don tabbatar da cewa ana binciken kwa-kwaf a kan cin zarafin mata da fyade da sauran miyagun ayyukan zaluncin nuna karfi a kan ’ya’ya mata da kananan yara da kuma tabbatar da ana hukunta wadanda duk aka samu da laifi. Kazalika ya kuma kafa Kwamitin bayar da shawara da jagoranci a kan irin wadancan mutane da aka zalunta, don tabbatar da cewa zaluncin da aka yi musu, bai sa sun shiga wani mawuyacin halin rayuwa ba a sanadiyar abin da aka yi musu din (kamar haukacewa ko makamancin hakan). A zamaninsa ya kafa Kwamiti ko Zauren sulhi don sasanta al’umma, kwamitin da ya kunshi malaman addinai da ’yan sanda da sauran masu ruwa da tsaki. Babban aikin da ya dora wa Zauren shi ne yadda zai rinka sasanta al’umma ko mutum da mutum da suka samu sabani ko wani rikici ko batun bashi, har ma da rigingimu irin na siyasa da na addini, duk dai da aniyar ganin ana zaune lafiya a Jihar Kano.
Kusan dukkan manya-manyan masu safarar miyagun kwayoyi zuwa Kano, sai da AIG Musa Katsina ya kama su tare da miyagun kwayoyinsu da darajarsu ta kai Nara biliyan 31da miliyan 800, wadanda ya tabbatar an hukunta su. Nuna godiya da samun wadannan nasarori ne, ya sanya da sahalewar Mai martaba Sarkin Kano, Hakimin Doguwa kuma Gado da masun Kano Alhaji Aliyu Harazumi ya nada AIG Musa Katsina a zaman Sarkin yakin Dajin Falgore, dajin da aka ce sama da shekaru 30, ba a samu wata hukumar tsaro da ta tunkare shi, ta kuma shige kamar yadda AIG Musa Katsina ya shige shi ya kuma yi nasara.
Ina ga da wannan hobbasa ta AIG Musa Katsina da kuma zargin da ya biyo baya, ba abin da ya fi dacewa sai Gwamnatin Jihar Kano ta hannum Kwamishinan kananan Hulumomin jihar Alhaji Murtala Sule Garo, wanda shi ke shugabantar kwamitin da gwamnatin ta dora wa alhakin ya karbi shanun daga ’yan sanda, ya kuma mayar da su ga masu su, ya fito ya yi wa duniya cikakken bayanin gaskiyar al’amari. Ita ma gwamnatin trayya akwai rawar da za ta taka don tabbatar da adalci. Barin a jira rahoton da sabon Sufeto Janar Alhaji Ibrahim Kpotu Idris zai fitar, wanda dama a karkashin kulawarsa tsohon Sufeto Janar Mista Solomon Arase ya kafa wancan kwamitin bincike da ke karkashin jagorancin tsohon mataimakin Sufeto Janar mai kula da shiyya ta daya da ke Kano, wanda a yanzu shi ne sabon mukaddashin Sufeto Janar mai kula da fannin mulki da kudi, kuma na biyu a cikin ’yan sandan kasar nan Alhaji Sha’aibu Gambo, ya fito da rahotansa, ko kusa ba zai sa AIG Musa Katsina ya samu adalci ba. Don kuwa kwamitin a cikin aikinsa ya ziyarci dukkan wuraren da ake zargi AIG Katsina ya mallaki kaddarori irin su gidaje ko gona, ba tare da ya nemi jin ta bakinsa ba. Tun daga nan mai karatu kasan wani ke neman ganin bayansa. Allah Ya kiyaye.
Wane ne ke son ganin bayan mataimakin Sufeto Janar Muhammad Musa Katsina?
A ’yan kwanakinnan labarai sun bayyana daga wata kafar yada labarai mai zaman kanta a Kano, da ta yi shaguben ana binciken wani babban jami`in…